Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya kaddamar da Shirin Sake Tsugunar da Al’ummar Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, biyo bayan alkawarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi na sake gina yankin bayan hatsarin jefa bam na soji bisa kure da ya faru kimanin shekaru biyu da suka gabata.
Shirin ya ƙunshi gidaje 133 da aka kammala, cibiyoyin ilimi da sauran muhimman gine-gine na zamani, domin dawo da mutunci, kwanciyar hankali da rayuwa mai inganci ga al’ummar da abin ya shafa.

Da yake jawabi yayin bikin kaddamarwar, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce aikin wata shaida ce ta cika alkawarin da Shugaba Tinubu ya dauka, yana mai jaddada cewa Gwamnatin Tarayya ba ta watsar da ‘yan ƙasa a lokutan ƙunci. Ya ce shirin wata hanya ce ta dawo da fata, zaman lafiya da hanyoyin samun abin rayuwa ga iyalan da rikici ya shafa.

Sanata Shettima ya bayyana cewa shirin na gudana ne a ƙarƙashin Shirin Sake Tsugunar da Mutanen da Rikici Ya Shafa, tare da tabbatar da cewa makamantan ayyuka suna gudana a wasu jihohi da suka haɗa da Kaduna, Kebbi, Sokoto, Zamfara, Niger, Katsina da Benue.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa nuna tausayi da ɗaukar mataki cikin gaggawa, tare da jinjinawa Mataimakin Shugaban Ƙasa kan rawar da ya taka wajen tabbatar da nasarar sake gina Tudun Biri.
Haka zalika, Darakta Janar ta Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), Zubaida Umar, ta ce aikin yana ɗaya daga cikin muhimman matakan Gwamnatin Tarayya na dawo da mutunci da damar ci gaba ga al’ummomin da bala’o’in jin ƙai suka shafa, a ƙarƙashin Ajandar Sabon Fata ta Shugaba Tinubu.

Jam’ar garin na Tudun Biri sun nuna godiya ga Gwamnatin Tarayya bisa wannan tallafi, suna mai cewa shirin ya dawo musu da fata da damar fara sabuwar rayuwa.

