Mazauna Sokoto Sun Yi Murna Bayan Nasarar Kashe Fitattun ‘Yan Bindiga 3 A Jihar

Al’ummar kauyukan da ke Mallamawa da Mazau a yankin Tsamaye/Mai Lalle dake Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto, sun yi murna da farin ciki bayan nasarar da sojojin hadin gwiwa na ‘Operation FANSAN YAMMA (OPFY)’ suka yi na kashe manyan shugabannin ‘yan bindiga uku a yankin.

A cewar jami’in watsa labarai na OPFY, Kyaftin David Adewusi, sojojin ya yin kai hari sun yi nasarar kashe Kachalla Nagomma, Gurmu da Ali Ɗan Dari biyar, sun kuma ƙwato bindigu ƙirar AK-47 guda uku da makamai da babura a hannun su.

Ya bayyana cewa ’yan ta’addan da mabiyansu sun shiga yankin ne don karɓar kuɗaɗen fansa da harajin da suka ƙaƙaba wa mazauna, kafin sojoji su tare su.

Kyaftin Adewusi, ya ce wannan nasara ta haifar da farin ciki da nutsuwa a tsakanin mutanen Mai Lalle, Tsamaye da Rimaye da wasu ƙauyuka a Sabon Birni da Goronyo, waɗanda suka daɗe suna fama da hare-haren ‘yan bindigar da aka kashe.

Ya kara da cewa OPFY na ci gaba da jajircewa wajen dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma da wasu sassan Arewa ta Tsakiya. Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai na sirri domin taimakawa nasarar ayyukan tsaro a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *