Ministan Yaɗa Labarai ya taya gidan rediyon Zuma FM Suleja murnar cika shekara 20 tare da haɓaka aikin gona

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya taya gidan rediyon Zuma 88.5 FM da ke Suleja a Jihar Neja murnar cika shekara 20 da kafuwa, tare da zagayowar karo na 9 na Bikin Girbin Noma na Zuma.

Zuma FM Suleja takan mai da hankali ne wajen ba da labaran aikin gona, kuma takan shirya bikin baje-kolin kayayyakin aikin gona a duk shekara.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a yau Asabar, Idris ya ce wannan cika shekara ta 20 wani muhimmin mataki ne wanda “ba wai murnar doguwar ɗorewar ku kawai ba ce, har ma shaida ce ta ƙarfin hangen nesan ki, daidaito, da hidimar al’umma.”

Ya ƙara da cewa: “A matsayin ta na tashar rediyo mai zaman kan sa ta farko a Jihar Neja, Zuma FM ta taka rawar gani a tarihi wajen faɗaɗa samun bayanai, ƙarfafa muryoyin al’ummomin karkara, da haɓaka sadarwar noma ta hanyoyin da ke ci gaba da inganta rayuwar al’umma a Arewa.

“Ƙudirin ku na tasirin zamantakewa da bunƙasa karkara yana wakiltar ainihin ma’anar watsa shirye-shirye mai ɗa’a.”

Ministan ya yaba wa shugabanni, ma’aikata da abokan hulɗar gidan rediyon waɗanda suka ɗore da wannan aiki nasu tsawon shekaru ashirin, yana mai cewa: “Ayyukan ku sun yi daidai da ƙoƙarin mu na ƙasa wajen gina Nijeriya mai wayewa, haɗin kai, da cigaba.

“Ina taya ku murna karo na biyu bisa wannan muhimmin biki. Ina sa ran kasancewa tare da ku a wannan tarihi mai muhimmanci.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *