A ci gaba da aiwatar da tsarin tallafin kuɗin karatu da Gwamnatin Tarayya ke bayarwa ta hannun Hukumar NELFUND, Jami’ar Maiduguri ta bayyana cewa ta karɓi kuɗi har Naira biliyan ɗaya da miliyan dari shida da sittin da uku da dubu ɗari huɗu da saba’in da biyar da naira dari biyar (N1,663,475,500) domin biyan kuɗin zangon karatu na shekarar 2024/2025. Wannan tallafi ya shafi ɗalibai 17,547 da ke karatu a jami’ar.
Cikin wata takarda da Jami’ar ta aikewa hukumar NELFUND wadda Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Mohammed Laminu Mele, ya sanya wa hannu, an bayyana godiya ga gwamnatin tarayya bisa wannan matakin da aka ce zai rage wa ɗalibai da iyayensu nauyin biyan kuɗin karatu. Takardar ta kuma nuna cewa an riga an karɓi kuɗin ne domin tabbatar da cewa babu ɗalibin da zai fuskanci tsaiko wajen cigaban karatunsa.
Wannan na daga cikin matakan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke dauka don saukaka damuwar ɗalibai a fannin ilimi tare da tabbatar da cewa kowa ya samu damar karatu ba tare da cikas ba. Hukumar NELFUND ta ce za a ci gaba da biyan sauran makarantun da suka cika sharudda, domin aiwatar da wannan tallafi a matakin ƙasa baki ɗaya.