Hukumar Bashi ta Daliban Najeriya (NELFUND) ta bayyana cewa tana kammala shirye-shiryen bude wata manhajar neman aiki domin ba wa masu cin gajiyar bashin damar samun aikin yi cikin sauki, a gida da kasashen waje.
Manajan Darakta na NELFUND, Akintunde Sawyerr ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Abuja don bikin cika shekara daya da fara aikin hukumar. Ya ce shirin zai fara aiki a shekarar 2026, kuma zai hada da jerin guraben aiki daga bangarorin gwamnati da masu zaman kansu da kuma kamfanonin kasa da kasa da ke da niyyar daukar ma’aikata daga Najeriya.
Sawyer ya bayyana cewa dalibai ba za su fara biyan bashin da suka karba ba har sai sun samu aiki, kuma biyan zai fara ne bayan kammala hidimar kasa (NYSC). Ya ce, “idan ba ka da aiki, ba za ka biya komai ba. Idan kuma ka samu aiki, za a cire kashi 10 cikin dari na albashinka kai tsaye a kowane wata.”
Idan aka sallami ma’aikaci ko ya ajiye aikinsa, cire kudin zai tsaya. Idan kuma wanda ke bin bashi ya rasu, za a goge bashin gaba daya ba tare da matsa wa iyalansa ba.
Kazalika, ya bukaci makarantu da su mayar da kudaden da dalibai suka biya da kansu kafin NELFUND ta aika kudin su. Ya ce makarantu na jan ƙafa wajen maidowa dalibai wadannan kudade. Hukumar ta ce ta samu koke-koke da dama daga dalibai, kuma hukumomin bincike kamar ICPC da EFCC sun shiga tsakani don tilasta wa wasu makarantu da suka ki maidowa dalibai hakkokinsu. A cewar Daraktan Ayyuka na NELFUND, Mustapha Iyal, hukumar na da bayanan dalibai fiye da miliyan 3.2 a tsarin ta, kuma tana sa ran sabbin aikace-aikace miliyan daya kafin karshen shekarar 2025 domin rage yawan ficewar dalibai daga makarantu saboda karancin kudi.