Nijeriya na ƙarfafa hulɗa da ƙasashen duniya don ƙaryata labaran ƙarya – Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na ƙarfafa hulɗa da abokan ta na ƙasashen duniya domin yaƙar labaran ƙarya da ake yaɗawa don ɓata sunan Nijeriya.

Idris ya bayyana hakan ne a birnin London, ƙasar Birtaniya, a ranar Asabar, a taron yankin Birtaniya na ‘Renewed Hope Global Dialogue’ mai taken, “Ƙarfafa Hulɗa da Duniya Don Sabunta Tattalin Arziki da Kyautata Martabar Ƙasa a Ƙarƙashin Shirin Sabunta Fata,” inda ya jaddada cewa haɗin gwiwa shi ne mabuɗin sake fasalta yadda ake kallon Nijeriya a idon duniya.

Ministan ya nuna yadda Nijeriya take fuskantar barazanar labaran ƙarya da ake yaɗawa game da ita na cewar wai gwamnati tana kai hari ga mabiya wasu addinai a ƙasar.

Ya ce: “Mun mayar da martani sosai, mun bayyana a sarari cewa waɗannan labaran ƙarya ne daga waɗanda ba su da masaniya kan Nijeriya. Muna buƙatar abokan mu na ƙasashen duniya da suka fahimci ƙasar mu su taimaka wajen yaɗa batutuwan gaskiya game da Nijeriya.”

Ya bayyana cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR), ta ƙaddamar da Ƙungiyar Kula da Martabar Nijeriya (NRMG) don inganta alfahari na ƙasa da kyakkyawan suna a duniya.

NRMG ta ƙaddamar da Aikin Kula da Martabar Nijeriya a Duniya, wanda ƙwararrun masu tsara suna ke jagoranta, inda ƙarin bayani zai biyo baya a watanni masu zuwa.

Ministan ya ce a ranar 15 ga Oktoba za a ɗauke ta a matsayin Ranar Martabar Nijeriya domin wayar da kan jama’a kan muhimmancin martabar ƙasa.

Ya jaddada cigaban da Nijeriya take samu a fagen diflomasiyya, inda ya ce ƙasar za ta gudanar da taron Ƙungiyar Hulɗa da Jama’a ta Afrika (APRA) 2026 da kuma Taron Duniya na Hulɗa da Jama’a (WPRF 2026) a Abuja — ita ce ƙasar Afrika ta farko da za gudanar da duka tarukan na duniya guda biyu a shekara guda.

Idris ya bayyana cewa manufofin diflomasiyyar Nijeriya, ƙarƙashin ƙa’idar Tinubu ta Dimokiraɗiyya, Cigaban Ƙasa, Yawan Jama’a, da ‘Yan Ƙasar Waje (4Ds), suna haifar da sakamako mai ma’ana.

Daga cikin su akwai shigar Nijeriya a matsayin ƙasar haɗin gwiwa ta BRICS, zaɓen ɗan Nijeriya a matsayin Sakatare-Janar na Ƙungiyar Ƙasashe Masu Fitar da Gas (GECF), da cire Nijeriya daga FATF Grey List, wanda ke nuna nasarorin shugabancin Bola Ahmed Tinubu.

A fannin cikin gida, Idris ya bayyana hoɓɓasan gwamnatin na kawo sauye-sauye, ya nuna cewa a yanzu Nijeriya tana aiwatar da tsarin haɗaɗɗen canjin kuɗi, da shirin lamuni da ya amfani ɗalibai fiye da rabin miliyan, da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa, da sabon tsarin lamunin sayen kayan masarufi, da shirin shugaban ƙasa na iskar gas, da sababbin dokokin haraji guda huɗu, da Hukumomin Raya Yankuna guda biyar, da kuma ƙirƙiro Ma’aikatar Raya Kiwon Dabbobi ta Tarayya.

Ya jaddada cewa waɗannan shirye-shirye ne da ke inganta burin ƙasar na zama mai ƙarfi ta fuskar tattalin arziki a duniya.

Ya ƙara da cewa Nijeriya tana dawo da martabar ta a gida da waje ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya jaddada cewa za ta ci gaba da ƙarfafa hulɗa da abokan haɗin gwiwa domin tabbatar da cigaban da ake samu.

“Mu gwamnati ce mai sauraren jama’a da kuma aiki tare, muna gayyatar ku da ku nemi ƙarin bayani game da abubuwan ban-sha’awa da ke faruwa a Nijeriya kuma ku duba hanyoyin haɗin gwiwa da mu don ɗaga sauye-sauyen da ake yi a Nijeriya zuwa mataki na gaba,” inji Idris.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *