Ashafa Murnai Barkiya
Mai Martaba Sarkin Kano, kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Muhammadu Sanusi Lamido, ya yaba wa hukumomin kula da harkokin kuɗi bisa matakan gaggawa da suka ɗauka wanda ya taimaka wajen daidaita tattalin arzikin Nijeriya a cikin shekarar da ta gabata.
Sanusi ya ce a baya ƙasar ta fuskanci mummunan rashin daidaiton tattalin arziki sakamakon yawan kuɗi a cikin tattalin arziki da kuma rashin kulawa wajen ƙara yawan kuɗin da ake fitarwa.
A cewar sa, Babban Bankin Nijeriya ya shafe kusan shekara guda yana ƙoƙarin cire yawan kuɗin da ya yi yawa daga cikin tsarin tattalin arziki domin dawo da daidaiton tattalin arziki.
Ya ce, “Ba ni da komai face kalmomin yabo ga abin da Babban Bankin ya yi. Mun fito ne daga yanayi na matsanancin rashin daidaito sakamakon sassaucin manufofin kuɗi da ƙaruwa ba tare da tsari ba a yawan kuɗi, kuma CBN ya shafe shekara guda yana kwashe kuɗin da ya yi yawa daga tsarin.”
Duk da amincewa cewa har yanzu kuɗin ruwa ga masu karɓar lamuni a banki tana da tsada, Sanusi ya bayyana cewa tsauraran matakan da aka ɗauka sun taimaka wajen daidaita farashin musayar kuɗaɗe tare da hana ƙasar nan faɗawa cikin babbar matsalar tattalin arziki.
Ya ce, “E, ribar kuɗin ruwa tana da tsada, amma mun samu daidaito a farashin musayar kuɗaɗe. Mun tsallake siraɗin rugujewar tattalin arziki gaba ɗaya.”
Sanusi ya ƙara da cewa hauhawar farashi, duk da cewa har yanzu tana da yawa, tana raguwa idan aka kwatanta da shekarun baya. Ya kuma bayyana cewa ribar kuɗin ruwa kusan kashi 20 cikin 100, duk da kasancewar ta mai tsada, ta fi sauƙi idan aka kwatanta da matakan da suka yi tsanani a shekarun baya.
Ya kuma jaddada ingancin tsarin ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya, inda ya ce sun haura dala biliyan 40, lamarin da ke ƙara wa tattalin arzikin ƙasa kariya.
Game da bunƙasar tattalin arziki, Lamido ya ce Nijeriya ta samu ci gaban sama da kashi 3 cikin 100 a zangon farko na shekarar 2025 da kuma sama da kashi 4 cikin 100 a zangon na biyu, abin da ya nuna gagarumin sauyi.
Ya ce, “Wannan ne karon farko cikin dogon lokaci da tattalin arzikin ƙasa ke bunƙasa fiye da yawan al’ummar ƙasar.”
