Shugaba Tinubu ya amince da ba da Naira Biliyan 1.85 don tallafa wa ilimi da rayuwar Matan Chibok

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da bada tallafi na Naira biliyan 1.85 domin tallafawa ilimi da gyaran rayuwa ga Yan Matan Chibok da aka kubutar tun daga sace su a shekarar 2014, har zuwa shekarar 2027.

Bisa bayanin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, daga cikin ‘yan Chibok da aka kubutar, 108 na ƙarƙashin kulawar gwamnati, inda 68 ke karatu a Jami’ar Amurka ta Najeriya (AUN), dake Yola. Gwamnatin tarayya na ci gaba da biyan kudin makaranta, masauki da sauran hakkokin su.

An bayyana cewa shirin tallafin ya haɗa da, Kudin makaranta da masauki, Horar da Su sana’o’i da kayan fara aiwatarwa, Tallafin lafiyar kwakwalwa da ta jiki, Tallafin iyaye da yara, Kula da ci gaban karatu. Jimillar dukkan waɗannan tsare-tsare ya kai N1,854,277,768.

Ma’aikatar ta ce shirin ba wai tallafi na kudi kawai ba ne, yana nuna ƙudurin Najeriya na mayar da wannan munanan lamari cikin labarin jarumta, mutunci da kyakyawan fata. Haka zalika, ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya nuna shugabanci nagari ta hanyar tabbatar da ci gaba da karatun ‘yan Matan Chibok a AUN duk da ya sami suka daga wasu ‘yan siyasa.

Tuni shekaru fiye da goma suka wuce tun lokacin da Boko Haram suka sace dalibai 276 daga Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Chibok, Borno, yayin da suke shirin kammala jarabawar karshe. Ya zuwa yanzu, fiye da 178 sun samu kubuta ko sun tsere, amma fiye da 90 har yanzu ba a san inda suke ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *