Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan dokar kafa cibiyoyin horas da ‘yan sanda a Najeriya

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokar kafa Cibiyoyin Horas da ‘Yan Sanda, wadda aka amince da ita a shekarar 2024 domin ba wa cibiyoyin horaswa na ‘yan sanda doka da cikakken tsarin aiki. Dokar ta ba da sahalewar doka ga cibiyoyi 48 na horaswa da ke fadin ƙasar tare da gina tsarin koyarwa, bincike da horaswa da zai tabbatar da ingantaccen aiki da bin ƙa’idodin duniya a harkar tsaro.

An kafa dokar ne bisa ƙudurin Sanata Ahmed Malam-Madori (na jam’iyyar APC mai wakiltar Jigawa Arewa Maso Gabas), wanda ya bayyana cewa manufar ita ce inganta ilimi, kwarewa da gogewar aikin ‘yan sanda.

Dokar ta tanadi nau’ukan cibiyoyi guda biyar da suka haɗa da Kolejojin ‘Yan Sanda, Makarantun Horaswa, Makarantun Dabarun Aiki, Makarantun Fasaha, da Cibiyoyi na Musamman. Wasu daga cikin fitattun cibiyoyin da dokar ta amince da su sun haɗa da Kolejin ‘Yan Sanda ta Ikeja, Kaduna, Maiduguri, Jos, Oji River, da Kwalejin bincike ta Enugu.

Haka kuma, dokar ta amince da cibiyoyin horaswa a Bauchi, Minna, Sokoto, Benin, Calabar, Ilorin, Ibadan, Jos, da wasu wurare don fadada horaswa a matakin ƙasa.

A karkashin dokar, Makarantun Dabarun Aiki za su rika koyar da dabaru na musamman ga rukunin “Mobile Police” da “Counter-Terrorism Unit”, inda aka amince da makarantun a Gwoza, Ila-Orangun, Ende-Hill, Nonwa-Tai, da Gombe. Haka nan akwai makarantun a Kafin Hausa, K9 School a Bukuru, da Mounted Troop School a Jos.

Sanata Malam-Madori ya bayyana amincewar Shugaba Tinubu da dokar a matsayin mataki mai girma da zai sauya tsarin tsaro a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *