Shugaba Tinubu ya sauya sunan Jami’ar Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Tarayya Azare zuwa Jami’ar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da sauya sunan Federal University of Medical Sciences, Azare zuwa Sheikh Dahiru Usman Bauchi University of Medical Sciences, Azare, domin girmama marigayi fitaccen malami kuma dattijo a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Sanarwar sauya sunan jami’ar ta zo ne a matsayin girmamawa ga irin rawar da marigayin ya taka wajen yaɗa ilimin addini, tarbiyya da zaman lafiya a Najeriya da ma ƙasashen waje.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya shahara wajen koyar da ilimi, da’awa da kuma tsayawa kan gaskiya da hadin kan al’umma.

A cewar Shugaban Ƙasa, wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na karrama manyan ’yan Najeriya da suka sadaukar da rayuwarsu wajen hidimar al’umma da ci gaban ƙasa, musamman a fannonin ilimi da tarbiyya.

Sauya sunan jami’ar ba zai shafi tsari da ayyukan karatu da koyarwa ba, sai dai zai ƙara wa cibiyar daraja tare da ɗora mata nauyin ci gaba da riko da kyawawan halayen da marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya tsaya a kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *