ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Labarai

Tsare-tsaren Daƙile Hauhawar Farashi: Yadda farashin kayan abinci ke sauka a kasuwannin karkara

Ashafa Murnai Barkiya

Bisa la’akari da yadda farashin kayan abincin da ake nomawa cikin ƙasa ke ci gaba da sauka, wakilin mu ya bibiyi yadda farashin wasu kayan abinci ya kasance a ranakun Laraba da Alhamis, kamar yadda ya ji daga bakin wani ɗan kasuwar hatsi mai suna Sama’ila Bello, ta garin Giwa, cikin Jihar Kaduna.

Ya shaida cewa kasuwar Giwa babbar kasuwar amfanin gona ce da ke ci a ranakun Alhamis da kuma Lahadi. Amma dai ta fi cika maƙil a ranar Alhamis.

“Masu sayen hatsi na zuwa tun daga kudancin ƙasar nan har Arewa daga Nijar da wasu ƙasashe. Ina tabbatar maka cewa ana lodin har kowar wake daga nan Giwa zuwa Nijar, Mali, Libiya har cikin Aljeriya.

Dangane da samun sauƙin farashi a wannan shekarar kuwa, ya shaida cewa an fara samun rangwamen tsadar kayan abinci tun bayan da Gwamnatin Tarayya ta ɗage harajin shigo da kayan abinci daga waje, da nufin a samu raguwar farashi.

Sama’ila wanda har farashin yake wallafawa a shafin sa Facebook, ya bayyana dalla-dalla yadda farashin kayan abinci ya kasance a kasuwar Giwa ta ranar Alhamis da kuma kasuwar Maƙarfi ta ranar Laraba, kamar haka:

Farashin Kayan Abinci A Kasuwar Giwa: 20 ga Nuwamba 2025

Farashin hatsi daga kasuwar hatsi ta giwa.

1.Farar Masara: Buhu ɗaya ya kama daga Naira 29,000, Naira 30,008 zuwa Naira 31,000.

  1. Farin Wake: An sayar da buhu ɗaya na farin wake kan — Naira 90,000 zuwa Naira 93,000, Naira 95,000 zuwa Naira 96,000.

3.Farashin Buhun Dawa: Ya kama daga Naira 27,000 zuwa Naira 29,000.

  1. Farashin Buhun Jar Masara: Ya kama dga Naira 29,000k har zuwa Naira 32,000.

5.Farashin Buhun Waken Soya: Ya kama daga Naira 50,000, 51,000 zuwa Naira 53,000.

  1. Shinkafa Samfarera Mai’Ɓawo: Buhu ɗaya ya kama daga Naira 28,000 zuwa Naira 30,000.
  2. Farashin Jan Wake: An saida buhu ɗaya na jan wake kan Naira 105,000 har zuwa Naira 115,000.
  3. Farashin Dauron Gero: An sayar da buhu ɗaya na gero dauro kan Naira 45,000 zuwa Naira 46,000.
  4. Farashin Buhun Gero Game-gari: An sayar da duk buhu ɗaya kan Naira 39,00 har zuwa Naira 42,000.
  5. Farashin Wake Mai Baƙin Hanci: Duk buhu ɗaya an sayar da shi kan Naira 105,000 zuwa Naira 110,000.
  6. Farashin Sabon Farin Wake: An sayar kan duk buhu ɗaya daga Naira 60,000 zuwa Naira 65,000.

Babu tsayayyen farashi, domin farashin ya riƙa canjawa ne ya danganta ga kyau da nagartar hatsin. Shi ya sa wani farashin ya fi wani.

Idan aka kwatanta wannan farashi da na kasuwar Maƙarfi da sauran kasuwanni a Arewacin Nijeriya, za a ga bambancin tsakanin nan da can ba shi da wata rata sosai.

An fara samun sauƙin abinci tun bayan da Babban Bankin Nijeriya CBN ya shigo da tsare-tsaren rage raɗaɗin tsadar rayuwa, kuma Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harajin kayan abincin da ake shigowa da su daga waje.

Sai dai ana hasashen daga watan Maris kayan abincin na iya ɗan tashi, amma ba can sama sosai ba.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *