Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na jagorantar zaman Majalisar ‘Yan Sanda ta Ƙasa a zauren majalisar da ke fadar shugaban ƙasa, Abuja. Zaman ya fara ne da ƙarfe 2:39 na rana a yau Alhamis, jim kaɗan bayan Shugaban Ƙasa ya kammala taron Majalisar Ƙoli ta Ƙasa inda ya gabatar da sunan wanda zai aka zaba a matsayin sabon shugaban INEC.
Taron ya zo ne makonni biyar bayan da Shugaban Ƙasa ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya tana nazarin batun kafa rundunar ‘yan sanda na jihohi, tare da ƙarfafa sabbin jami’an tsaron daji (forest guards) da aka tura cikin dazuzzuka domin yaki da matsalar tsaro. A ranar 2 ga Satumba, 2025, yayin da ya karɓi tawagar jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Radda, Shugaba Tinubu ya ce: “Ina duba dukkan fannoni na tsaro; dole ne in samar da rundunar ‘yan sanda ta jihohi.”
A yayin zaman na yau, mahalarta sun yi addu’a domin tunawa da tsohon Sufeton ‘Yan Sanda na Ƙasa, Solomon Arase, wanda ya rasu a ranar 31 ga Agusta, 2025. Majalisar ta yi nazari kan kalubalen tsaro na yanzu, cigaban da aka samu a gyaran da akai a hukumar ‘yan sanda, da kuma harkokin jin daɗi da albarkatun jami’ai a fadin ƙasar. Haka kuma, ana sa ran za a tattauna batutuwa da suka shafi shugabanci da tsarin aiki tsakanin jihohi.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, Sakataren Gwamnatin Ƙasa George Akume, Mai ba da shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, da Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Ibrahim Gaidam na cikin mahalarta zaman, tare da dukkan gwamnonin jihohi da wakilan su. Majalisar ‘Yan Sanda, wacce kundin tsarin mulki ya kafa ƙarƙashin sashe na 153, tana ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa, kuma tana ba da shawara kan tsari, gudanarwa da kula da rundunar ‘yan sanda, har ma da batun nada ko cire Sufeton ‘Yan Sanda na Ƙasa.
