Ministan Yaɗa Labarai ya yi alhinin ‘yan jarida bakwai na Gombe da suka rasu a haɗarin mota
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana matuƙar kaɗuwa da alhini kan rasuwar wasu ‘yan jarida bakwai a wani mummunan haɗarin mota guda ɗaya da ya faru a yankin Gombe ta Kudu, Jihar Gombe, a ranar Litinin. Lamarin ya faru ne da yammacin Litinin yayin da ‘yan jaridar suke dawowa…
Gwamnatin Tarayya ta jaddada ƙudirin bin doka da oda, kuma ta yi watsi da zargin kai wa ‘yan adawa hari
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba ta da wani shiri na kamawa ko tsare ko gurfanar da ’yan adawa ba bisa ƙa’ida ba. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka a cikin sanarwar da ya bayar a ranar Talata sakamakon ɓullar wata takardar bogi da ke yawo…
Sojoji sun hallaka ‘yan ta’adda sama da 80, sun ceto mutane 34 a jihohi da dama
Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ta sanar da cewa dakarunta sun hallaka ‘yan ta’adda sama da 80, tare da ceto mutane 34 da aka sace, a jerin hare-haren haɗin gwiwa da aka gudanar tsakanin ranakun 25 zuwa 29 ga Disamba, 2025. Wata majiya mai tushe daga Hedkwatar Sojin Ƙasa ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai…
Bankwana Da 2025: Yadda CBN ya hana ‘yan Nijeriya fuskantar ƙarancin kuɗi a ATM da bankuna yayin hutun ƙarshen shekara
Ashafa Murnai Barkiya ’Yan Nijeriya a faɗin ƙasar nan sun gudanar da hadahadar kuɗaɗe cikin sauƙi a lokacin Kirsimeti na 2025. Har zuwa ranar 28 ga Disamba, babu rahotannin samun cikas ko ƙarancin kuɗi a ATM da bankuna a faɗin ƙasar nan. Yayin da matsalar ƙarancin kuɗi ta addabi bukukuwan Kirsimeti na bara, a bana…
Gwamnati Ta Kammala Horar da Sama da Matasa 7,000 a Matsayin Masu Tsaron Daji Da Za a Tura su Aiki Nan take
Gwamnatin Tarayya ta sanar da kammala horar da fiye da matasa 7,000 da aka dauka a matsayin Masu Tsaron Daji (Forest Guards) a jihohi bakwai da ake ganin suna fuskantar matsanancin barazanar tsaro. Wannan horo ya gudana ne karkashin shirin Presidential Forest Guards Initiative da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya kaddamar a watan Mayu…
YADDA MU’UTAMAR NA MANYAN ƊALIBAN FUDIYYA (FOSA), 2025. YA GUDANA A KADUNA
Daga Hafiz Nura Alja’afaree Roni. Dandalin manyan Ɗaliban Fudiyya (FOSA) sun gudanar da gagarumin Mu’utamar na kwanaki uku cikin nasara da tsari a muhallin Makarantar Imam Sadiq (as) da ke Nassarawa, Kaduna. Taron ya tattaro manyan ɗalibai fudiyya daga sassa daban-daban na ƙasa domin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ilimi, tarbiyya, Inganta Fudiyyoyi da…
Gwamnatin Najeriya Da Amurka Sun Kai Hari Kan ’Yan ISIS A Dajin Bauni Da ke Jihar Sokoto
Gwamnatin Najeriya ta sanar da nasarar kai hare-haren da aka tsara cikin tsanaki kan wasu manyan sansanonin ’yan ta’addan ISIS guda biyu da ke cikin dajin Bauni, a ƙaramar hukumar Tangaza ta Jihar Sokoto. A cewar sanarwar da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta fitar, an gudanar da harin ne tare da haɗin…
SHUGABA TINUBU YA YI ALHININ RASUWAR ’YAN MAJALISAR KANO BIYU
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga Gwamnati da al’ummar Jihar Kano bisa rasuwar ’yan Majalisar Dokokin jihar guda biyu. Marigayan su ne Aminu Sa’ad Ungogo da Aliyu Sarki Daneji, wakilan mazabun Ungogo da Kano Municipal, waɗanda suka rasu a lokuta daban-daban cikin awa ɗaya a ranar Laraba. Shugaba Tinubu ya bayyana…
Najeriya da Amurka Sun Kai Harin Hadin Gwiwa Kan Manyan Maboyar ’Yan Ta’adda a Arewa Maso Yamma
Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya ta tabbatar da cewa gwamnati na ci gaba da hadin gwiwar tsaro da kasashen duniya musamman Amurka domin dakile barazanar ta’addanci a kasar. Wannan mataki, a cewar ma’aikatar, ya haifar da samun karin nasarori a yunkurin kai hare-haren jiragen sama da suka yi a wasu sansanonin ’yan ta’adda a yankin…
