KARFAFA AL’UMMA: Gwamna Lawal Ya Raba Katin Cirar Kuɗi Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Zamfara
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ƙaddamar da rabon katunan cirar kuɗi ga waɗanda suka ci gajiyar shirye-shiryen tallafi na Bankin Duniya da ake kira ‘Cash Transfer’. An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a ranar Litinin a Sakatariyar Ƙaramar Hukumar Tsafe. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar…
