Sojojin Najeriya Sun Kashe Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda Da Aka Fi Sani Da ‘Dan Dari Biyar’ a Jihar Sokoto

Sojojin Najeriya da ke aiki ƙarƙashin rundunar Operation FANSAN YANMA sun samu nasarar kashe wani shahararren shugaban Ƙungiyar Ɓarayi mai suna Dan Dari Biyar a yayin wani samame da suka kai a yammacin karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto.

An kashe ɗan ta’addan ne ranar Alhamis, a lokacin da ya fito daga dajin Tidibale domin karɓar kuɗin fansa daga ‘yan uwan waɗanda suka sace.

Dan Dari Biyar ya shahara wajen zaluntar waɗanda ya kama, tare da ƙwace musu kuɗaɗe da cin zarafinsu kafin sako su.

Rahotanni sun ce wannan ɗan ta’adda ya kasance yana ɓoye ne a dajin Tidibale, inda yake fita kai hare-hare a ƙauyukan Lalle, Tsamaye da wasu sassa na Gwaronyo. An danganta shi da kai farmaki da kona kauyuka, musamman harin da ya kai Gidan Sale a hanyar Gundumi.

Haka kuma, bayanan leƙen asiri sun tabbatar da rawar da ya taka a wasu hare-hare da dama a yankin gabashin jihar Sokoto.

Wannan samame wani ɓangare ne na ci gaba da aikin kawar da ƴan ta’adda da rugujewa maboyarsu a jihar Sokoto. An kammala aikin ne ta haɗin guiwar sojojin Najeriya da ƴan sa-kai na cikin gida. Sojojin sun kwato bindigogi, harsasai da na’urorin sadarwa, yayin da ake ci gaba da farautar ragowar ƴan ƙungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *