CBN ya umarci bankuna su janye tallace-tallace masu ɗauke da ninanci da yaudarar kwastomomi

Ashafa Murnai Barkiya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi kakkausan gargaɗi tare da umartar dukkan bankuna, bankunan asusun ‘walet’ na biyan kuɗi da sauran cibiyoyin hadahadar kuɗi da yake kula da su, cewa su gaggauta janye duk wasu tallace-tallace ko wasu bayanai da ba su cika ƙa’idodin kare buƙatu da haƙƙin Kwastomomi bisa tsarin ingantacciyar hanyar tallata kaya ba.

CBN ya bada wannan umarni, a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis kuma Olubunmi Ayodele-Oni ya sanya wa hannu a madadin Daraktan Sashen Bin Doka na CBN, ya biyo bayan wani bincike na masana’antu da ya tabbatar cewa akwai bambance-bambancen fassarar da cibiyoyi ke yi dangane da buƙatun bayyana bayani, gaskiya da ingantacciyar tallatawa bisa Ƙa’idodin Dokar Kare Mabuƙata ta 2019 da Jagororin Tallace-Tallace na 2000 ga Cibiyoyin Ajiya.

Babban Banki ya ce binciken ya gano cewa har yanzu wasu cibiyoyi na tallata bayanan da ke kauce fa’ida fiye da gaskiya, rashin bayyana muhimman bayanai, ɓoye haɗari ko amfani da bayanan kuɗi da ba a tantance ba.

CBN ta gargaɗi cewa irin waɗannan halaye na yaudarar kwastomomi na ɓata gasa tsakanin bankuna da cibiyoyin kuɗi, kuma yana lalata amincin tsarin kuɗi.

Bankin ya jaddada cewa duk tallace-tallace dole ne su kasance na gaskiya masu ɗauke da cikakkun bayanai.

Sannan kuma ya haramta amfani da kalmomi masu kwatanta ninanci kai tsaye ko a kaikaice, misali, irin masu nuni da cewa “mu ne mafi”, “mun kowa”, ko kuma tallar da ke ɗauke ɓatanci ga wasu cibiyoyi.

Har yau dai, bankin ya haramta tallace-tallacen da ke amfani da tayin lashe kyauta da kaɗan-kaɗan ko zaɓen masu sa’a da sauran shirye-shiryen da ke tura mabuƙata su afkawa su shawarar zuba kuɗi ba tare da cikakkiyar fahimtar haɗarin da ke tattare da su ba.

A ƙarƙashin wannan sabuwar dokar bin tsare-tsaren, ya zama tilas bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi su tura cikakkiyar sanarwa ga CBN kafin a saki kowace talla ko wasu bayanan isar da saƙo.

“Sanarwar dole ne ta ƙunshi tsawon lokacin tallar, cikakken abin da za a wallafa ko watsawa, mutanen da ake son tallar ta kai gare su da kuma yankunan da aka yi niyyar sakon ya kai, tare da tabbaci a rubuce mai ɗauke da cewa sashen bin doka da na shari’a sun amince.

“Haka kuma dole ne cibiyoyin su gabatar da hujja cewa samfurin da suke tallatawa ya samu amincewar CBN tun da farko,” in ji sanarwar.

Bankin ya jaddada cewa wannan tsarin sanarwa ba yana nufin CBN ta amince da tallar ba, kuma har yanzu cibiyoyin kuɗi ne ke da cikakken alhakin tabbatar da bin doka da ƙa’idodi.

CBN ta umarci dukkan cibiyoyi su janye duk wata talla da ba ta cika ƙa’idoji ba nan take, tare da miƙa takardar tabbacin bin doka cikin kwanaki 30, wadda Shugaban Kamfani/Manajan Darakta, Babban Jami’in Bin Doka za su sanya wa hannu.

“Wannan takardar ta tabbatar da cewa dukkan tallace-tallace da dabarun yaɗa labarai na yanzu suna bin dokoki da ƙa’idodin da abin ya shafa,” inji sanarwar.

CBN ya kuma bayyana cewa daga watan Janairu 2026 za ta gudanar da wani bincike na gaba domin tantance yadda bankuna da cibiyoyin hadahadar suka yi biyayya da umarnin.

“Za a ci tarar duk wata cibiyar da aka samu tana karya dokokin, bisa ga Dokar BOFIA ta shekarar 2020 da Ƙa’idodin Kare Haƙƙin Kwastomomi.”

CBN ya bayyana aniyarta ci gaba da inganta bin tsare-tsare na gaskiya, bayyananniyar hulɗa da gudanar da hulɗa a bayyane bisa kyakkyawar hanyar talla a tsarin kuɗi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *