Fadar Shugaban Ƙasa Ta Karyata Jita-Jitar Hana Shettima Shiga Villa

Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta jita-jitar da ke cewa an hana Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, shiga fadar shugaban ƙasa. A wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaban Ƙasa kan harkokin watsa labarai a ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Stanley Nkwocha, ya fitar, ya bayyana cewa labarin karya ne marar tushe da nufin tada zaune tsaye da ɓata sunan gwamnati.

Sanarwar ta jaddada cewa babu wani lokaci da aka hana Shettima shiga Villa, kuma rahoton da wasu shafukan yanar gizo suka wallafa ba ya da wani tushe. Nkwocha ya bayyana lamarin a matsayin ƙoƙarin tada fitina da neman haifar da rikici tsakanin manyan shugabannin ƙasa.

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce dangantakar Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa na nan daram, inda suka gina haɗin kai da mutunta juna wajen cika alƙawuran da suka ɗauka ga ƴan Najeriya. Sanarwar ta kuma bukaci kafafen watsa labarai da su rika tantance gaskiyar labarai daga sahihan majiyoyi kafin wallafawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *