Ministan Sufuri na Ƙasa, Sa’idu Alkali, ya bayyana cewa aikin titin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Kano zai kammala nan da shekarar 2026, inda ya bayyana cewa aikin wanda ya tsaya a kashi 15 cikin 100 kafin zuwan gwamnatin Tinubu, yanzu ya kai kashi 53 cikin 100. Ya sanar da hakan ne yayin jawabin sa a taron tattaunawa tsakanin gwamnati da jama’a da Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation ta shirya a Kaduna.
Alkali ya ce yankin Arewa na daga cikin mafi yawan wadanda ke cin moriyar ayyukan ci gaban ababen more rayuwa na gwamnatin Tinubu karkashin shirin Renewed Hope Agenda. Ya kara da cewa aikin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi ya kai kashi 61 cikin 100, yayin da wasu sassa na aikin titin jirgin kasa daga Port Harcourt zuwa Maiduguri ke ci gaba da gudana.
Ya ce aikin manyan hanyoyi kamar Sokoto zuwa Badagry mai tsawon kilomita 1,068 wanda ya hada jihohi bakwai yana daga cikin manyan ayyuka da gwamnati ke aiwatarwa don bunkasa hadin kai da tattalin arzikin kasa. Hakazalika, an fara aikin gyaran layin jirgin kasa daga Legas zuwa Kano domin saukaka jigilar kaya.
A bangaren makamashi, Alkali ya bayyana cewa Hukumar Wutar Lantarki ta Karkara (REA) ta girka fiye da na’urorin hasken rana 1,100 da kuma gina ƙananan wurin samar da lantarki guda 32 a jihohin Arewa maso Gabas. Ya kara da cewa an gina gidaje fiye da 3,000 a jihohin Arewa karkashin shirin Renewed Hope Cities, kuma ana shirin kafa sabbin tashoshin sufuri a kowane yanki na na kasar nan.
