Ma’aikatar Tsaro Na Amfani Da Ofishin NSA Wajen Gallaza Wa ’Yan Adawa – Gwamnatin Zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwar ta kan abin da ta kira amfani da ƙarfin Gwamnatin Tarayya wajen gallaza wa da tsoratar da ’yan adawa a jihar, tana mai cewa wannan al’amari na barazana ga dimokuraɗiyya da tsarin doka a Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, gwamnatin ta ce ba ta da wani zabi face ta sanar da jama’a yadda Ƙaramin Ministan Tsaro ke amfani da ofishin Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara kan Tsaro, wato NSA, wajen gallaza wa ’yan adawa da gwamnati a Zamfara.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin ta samu labari mai tayar da hankali dangane da sace Saleem Abubakar, wanda ke aiki a matsayin Mataimaki na Fasaha a Ofishin Gwamnan Jihar Zamfara, inda aka ce an yi garkuwa da shi a birnin Abuja a ranar da ta gabata.

A cewar gwamnatin, wasu jami’ai na musamman daga ofishin NSA ne suka aikata wannan lamari ba tare da nuna wata takardar kama shi ba.

An ce an ɗauki Saleem Abubakar zuwa wani wuri da ba a bayyana ba, sannan aka riƙa ɗaukar sa daga wuri zuwa wuri domin boye sahun takamaiman inda yake.

Abin da ya fi tayar da hankali, a cewar sanarwar, shi ne yadda aka danganta wannan lamari kai tsaye da Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, wanda aka ce ya yi amfani da ofishin NSA wajen shirya wannan aiki.

Gwamnatin Zamfara ta bayyana hakan a matsayin wani lamari mai hatsari da ya kamata ’yan Nijeriya su yi Alla-wadai da shi baki ɗaya.

Sanarwar ta ce, yin amfani da manyan hukumomin tsaro na ƙasa wajen cin zarafin ’yan adawar siyasa abu ne da ke lalata amincewar jama’a ga tsaro, tare da jefa martabar ƙasa cikin haɗari.

Ta jaddada cewa babu wata matsala ko sabani da ya isa a tauye ’yancin ɗan ƙasa ko a karya doka ta hanyar sace mutum ba tare da bin hanyoyin shari’a ba.

Gwamnatin Zamfara ta yi kira ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya yi gaggawar bibiyar lamarin tare da kiran ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, tana mai gargaɗin cewa irin waɗannan ayyuka na iya janyo mummunan tasiri ga sunan Nijeriya a idon duniya.

Ta kuma ce idan har akwai wata zargi ko matsala da ake dangantawa da Saleem Abubakar, abin da ya dace shi ne a gurfanar da shi a gaban kotu bisa tanadin doka, ba wai a yi garkuwa da shi ko a tsoratar da shi ta hanyar ƙarfin tsaro ba.

A ƙarshe, gwamnatin jihar ta bayyana cewa tana sa ido sosai kan wannan lamari, tare da alƙawarin bin sa har ƙarshe domin tabbatar da cewa an yi adalci kuma an kare martabar dimokuraɗiyya da ’yancin ɗan Adam a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *