Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya sake jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na dawo da amincewar jama’a ga bayanan gwamnati, inda ya ce tsare gaskiya da muradin ƙasa za su ci gaba da zama jagora a ayyukan ma’aikatar sa.
Ministan ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a Abuja, lokacin da aka gudanar da bikin ba da kyaututtukan karramawa kan nagartar aiki na shekarar 2025 mai taken “Nigeria Excellence Awards in Public Service” (NAEAPS), inda ya karɓi Kyautar “Excellence in Public Communication and Transparency.”

Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya tare da haɗin gwiwar kamfanin The Best Strategic Media ne suka shirya bikin.
Wannan sabuwar lambar yabon ita ce ta biyu da Ministan ya samu cikin kwana biyar da suka gabata, bayan ya samu “Business Day Award for Excellence in Public Service” a ranar 3 ga Disamba.

Bayan karɓar lambar yabon, Idris ya bayyana cewa wannan yabo yana da muhimmanci sosai kuma yana ƙara masa ƙwarin gwiwa.
Ya ce: “Wannan ƙasa ta kowa ce, don haka a gane irin gudunmuwar da na bayar wajen cigaban ta abin farin ciki ne. Wannan yana ba mu ƙarin ƙarfi wajen yi wa ƙasa aiki.”
Ministan ya bayyana cewa umarnin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba shi a bayyane yake, kuma ma’aikatar sa ta jajirce wajen ƙarfafa sadarwar jama’a domin tallafa wa cigaban ƙasa.
Ya ce: “Za mu ci gaba da dawo da amincewa a sadarwar jama’a ta hanyar mu’amala ta gaskiya. Wannan na daga cikin manyan ƙalubale, kuma muna tunkarar sa bakin ƙarfin mu.”

Idris ya kuma jaddada ƙoƙarin ma’aikatar na yaƙi da labaran ƙarya inda ya gargaɗi cewa wannan barazanar tana iya kawo rashin daidaito a al’umma idan ba a kula da ita ba.
Ya ce: “Muna aiki tuƙuru don tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya suna samun sahihan bayanai. Labaran ƙarya da bayanai marasa tushe na iya gina ko rushe al’umma, don haka za mu ci gaba da tunkarar su ta hanyar sadarwa mai tsage gaskiya kuma a kan lokaci.”
Ministan ya bayyana cewa cigaban da aka samu zuwa yanzu sakamakon aiki tare ne, inda ya yaba wa shugabannin hukumomi, daraktoci, da ma’aikata a duk faɗin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai.
Ya ce: “Wannan yabo ba nawa ni kaɗai ba ne. Ya shafi kowa a ma’aikatar da ya yi aiki tuƙuru wajen sake fasalin fannin yaɗa labarai da sadarwa.”
Ministan ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su ci gaba da haɗin kai da jajircewa wajen gina ƙasa mai ƙarfi, inda ya ce: “Ba mu da wata ƙasa ta daban. Dole mu haɗa hannu don tafiyar da Nijeriya gaba. Ƙasar ta fi mu duka girma, kuma dole mu yi aiki tare domin cigaban ta.”
Daga cikin sauran waɗanda suka samu lambobin yabo a bikin akwai gwamnonin jihohin Bauchi, Zamfara, Kogi, da Inugu, da kuma Ministocin Sufuri, Harkokin Mata, da wasu fitattun ma’aikatan gwamnati daga faɗin tarayyar ƙasar nan.
