Ambaliyar Jebba Dam ta lalata gonaki hekta 1,094 da ke jihar Neja – Hukumar NEMA
Daga Abubakar Musa Ambaliyar ruwa daga Jebba Dam ta lalata gonaki 1,094 a al’ummu 32, inda hakan ya shafi manona 544 a karamar hukumar Mokwa da ke jihar Neja. Kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito, ambaliyar wadda ta faru ta shanye tare da lalata gonakin noman rani na shinkafa da ke bakin Rafin Neja wanda…
