Ƙarin Harajin mai na 5% ba sabon haraji ba ne, kuma ba za a aiwatar da shi yanzu ba
Kwamitin Shugaban Kasa kan Tsarin Haraji da Sauye-sauyen Haraji ya ce karin kashi 5% a kan farashin mai ba sabon haraji ba ne da gwamnatin Tinubu ta kawo. A cewar kwamitin, wannan kudiri daman akwai shi a cikin dokar Federal Roads Maintenance Agency (FERMA) ta 2007, sai dai an sake saka shi a sabuwar dokar…
