Gwamna Dauda Lawal ya sa hannu kan dokar taƙaita zirga-zirgar babura a jihar
Gwamna Dauda Lawal ya amince, tare da sanya hannu a dokar taƙaita zirga-zirgar babura a jihar Zamfara. A Alhamis ɗin nan ne gwamnan ya rattaba hannun a fadar gwamnatin jihar da ke Gusau. A cikin wata sanarwa da Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa Majalisar tsaro ta jihar ne…
