Ashafa Murnai Barkiya
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya bayyana irin gagarimar nasarar farfaɗo da tattalin arzikin Nijeriya da ya ce an samu daga hawan sa shugabancin bankin zuwa yanzu a ƙarshen 2025.
Ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi wurin taron cin abincin dare na shekara-shekara na Cibiyar Manyan Masu Hannu a Harkokin Banki ta Nijeriya (CIBN), ranar Alhamis a Legas.
A wurin taron wanda shi ne na 60, Cardoso ya jaddada cewa, “a daren yau, mun hallara a wani muhimmin lokaci ga ƙasar mu, wanda a daidai lokacin da duniya ke da rashin tabbas, lokacin da ake sake fasalin manufofi a gida, da lokacin da ake ci gaba da farfaɗo da muhimman cibiyoyi. Duk da ƙalubalen da ke fama da su da waɗanda ake fuskanta, mun samu sabon haske. A cikin shekarar da ta gabata mun dage wajen dawo da daidaiton tattalin arziki, gina amincewa, da ƙarfafa martabar Babban Bankin Nijeriya.
“Ina farin cikin sanar da ku cewa mun samu ci gaba mai ma’ana a waɗannan fannoni, duk kuwa da cewa muna sane da har yanzu akwai sauran ƙalubale a gaban mu. Mun tsaya kan abin da muka faɗa tun a farko. Wato abin da muka ce za mu yi, shi muke yi bisa tsari na gaskiya da daidaito.” Inji Cardoso.
Sannan kuma ya tunatar da matsalolin da al’umma da dama ke fuskanta a yanzu. Ya ce, “abubuwan da suka faru kwanan nan da kuma maida hankalin duniya kan batun tsaro, sun nuna mana tasirin da rikice-rikice ke yi ga mutane. A madadin Babban Banki, muna miƙa ta’aziyyar mu ga iyalai da al’umma da abin ya shafa.
“Ko da yake harkar tsaro ba ta cikin hurumin Babban Banki, amma muna sane da illolin ta ga tattalin arziki. Gwamnati na ɗaukar matakai, mu kuma a matsayin na masu kula da samar da daidaito a cikin kuɗi, muna tabbatar da cewa asasin tattalin arzikin ƙasa ya tsaya da ƙarfi domin zuba jari, rayuwar jama’a, da juriya su ci gaba da ƙarfafa yayin da ake ci gaba da shawo kan matsalolin tsaro.”
Cardoso ya fahimtar dangane da ci gaban Nijeriya a yau, inda ya ce tilas ne mu duba matsayin tattalin arzikin duniya, wanda ya cecya na tafiya cikin rauni saboda, rikice-rikicen siyasa, haka kuma ƙasashen masu ƙarfin arziki sun shiga yanayin raguwa, yayin da ƙasashe masu tasowa da dama, musamman a Afirka, ke fama da tsadar kuɗin waje da hauhawar farashi.”
Sai dai ya ci gaba da munin cewa, duk da wannan, akwai wuraren da aka samu sauƙi saboda raguwar darajar Dalar Amurka da saukar hauhawar farashi. Ƙasashe da dama a Afirka sun fara samun kwanciyar hankali a kuɗin su. Bugu da ƙari, Afirka ta Sub-Sahara na sa ran yin ci gaba da kashi 3.8% a 2025 da kashi 4.4% a 2026.
“Nijeriya, Habasha, da Côte d’Ivoire na jagorantar wannan farfaɗowa, sakamakon ingantattun tsare-tsaren gida, karfaffun cibiyoyi, da ingantaccen shugabanci.”
Daga Ina Zuwa Ina?
Ya ci gaba da cewa “lokacin da muka hau muƙami, Nijeriya na cikin matsaloli masu tsanani, kama dsga hauhawar farashi na tashi, ga shi a lokacin an yi fama da ƙarancin Dala a bankuna. Sannan akwai rashin amincewa ga manufofin tattalin arziki. Kuma an kauce daga tsarin kuɗi na zamani. Sannan shigo da kuɗi daga ɓangaren masu sha’awar zuba jari cikin Najeriya ya tsaya cak. Ita ma kasuwar musayar kuɗi ta durƙushe. Akwai kwantai na bashin biyan buƙatun masu neman dala sama da dala biliyan 7 da ba a biya ba. Tazarar farashin naira a kasuwannin hukuma da na bayan fage ta wuce zuwa fiye da kashi 60%.
“Hauhawar farashi ya kai kashi 34.6% a Nuwamba 2024. Farashin abinci ya matse al’umma, har an shiga ƙuncin rayuwa.”
Cardoso ya ce “wannan shi ne halin da muka samu Nijeriya, ba a bakin rami ba, amma a ciki tsundum.
Yadda Muka Ceto Tattalin Tattalin Arzikin Nijeriya:
Ya bayyana cewa cikin shekara guda, komai ya fara canzawa, yayin da ƙarfin tattalin arzikin cikin gida ya tashi zuwa kashi 4.23% a cikin watanni ukun tsakiyar shekarar 2025. Wannan kuwa shi ne mafi girma cikin shekaru huɗu.
“Hauhawar farashi ta ragu daga 34.6% zuwa 16.05% a Oktoba 2025, inda watanni bakwai a jere tsadar da hauhawar na raguwa.
“Hakan na dawo da ƙarfi da nauyin aljihun jama’a ya dawo har ake iya sayen kayayyakin biyan buƙatu na yau da kullum.
“Manufar mu ita ce mu ci gaba da rage hauhawar farashi. Mun inganta bayanai, mun ƙarfafa sadarwa, mun daina biyan gibin kuɗi ga gwamnati. A shekarar 2026 ana sa ran ci gaba da saukar farashi.
Gyaran kasuwar hadahadar kuɗaɗen waje na daga cikin gyare-gyaren da Cardoso ya ce ya yi tasiri sosai wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar nan.
“Mun wargaza tsofaffin hanyoyi da dama. Mun biya dukkan bashin kuɗaɗen waje ga masu neman musayar kuɗi na baya. An kafa dokar musayar kuɗaɗe, domin inganci da gaskiya. Naira yanzu tana cikin daidaitaccen matsayi, ta yadda tazarar ta da kasuwar bayan fage tana ƙasa da kashi 2%. Jarin waje ya kai dala biliyan 20.98 cikin watanni 10 na 2025.”
Cardoso ya sake tabbatar da cewa adadin kuɗin ajiyar waje ya kai Dala biliyan 46.7, wato mafi girma cikin kusan shekaru bakwai. Wannan ya zo ne ba ta hanyar basusuka ba, sai dai ta hanyoyin cikin gida da ƙaruwar fitar da kayayyakin da ba na mai ba.
Sannan ya ce a ƙoƙarin da CBN ke yi domin bunƙasa tattalin arziki ya kai geji da mizanin Dala tiriliyan ɗaya nan da 2030, tuni har an samu bankuna 16 waɗanda suka cika sharuɗɗan ƙara ƙarfin jarin su.
