ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Year: 2025

SHUGABA TINUBU YA SHA ALWASHIN SAMAR DA TSARO A AREWA MASO YAMMA

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana ƙudurin gwamnatinsa na ɗaukar matakin gaggawa wajen dawo da aminci a dazukan da ‘yan ta’adda suka mamaye a Arewa maso Yamma da sauran sassan ƙasar. Ya ce gwamnatinsa za ta ƙara ƙaimi sosai…

Gwamnatin Nijeriya Ta Goyi Bayan Amfani Da Ƙirƙirarrar Basira Cikin Ɗa’a A Aikin Jarida – Idris

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana ƙudirin ta na amfani da Ƙirƙirarrar Basira (AI) a aikin jarida cikin ɗa’a, tare da mayar da hankali kan ‘yancin faɗin albarkacin baki, bin ƙa’idojin aikin jarida da kuma koyar da jama’a ilimin kafafen watsa labarai….

Aikin Gina Tashar Jirgin Ƙasa A Kano Yana Ci Gaba Gadan-gadan

Aikin gina tashar jirgin ƙasa ta zamani a Kano, ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, yana ci gaba da tafiya babu kama hannun yaro. Kamfanin da ke gina tashar, wato CCECC na ƙasar Chana, ya bayyana a…

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabon shafin intanet don inganta sayayya a ma’aikatun gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin magance matsalolin da suka dabaibaye harkar sayayya a hukumomin gwamnati tare da ƙara inganta ayyuka a ma’aikatun gwamnati. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka a Abuja…

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima Ya Jagoranci Masu Tarbar Tsoho da Sabon Gwamnan Jihar Delta Zuwa APC

A wani Gangami na dubban jamaa,Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen tarbar gwamna Sheriff Francis Oborevwori na jihar Delta da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa da magoya bayansu wadanda suka yi ƙaura daga jam’iyyar PDP…

SHUGABAN KASA TINUBU YA YI ALHININ RASHIN MALAM MAINASARA HABIBI

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matukar kaɗuwarsa bisa rasuwar babban malamin addinin Islama na garin Zariya, Sheikh Mainasara Liman Habibi. Sheikh Habibi ya rasu a karshen makon da ya gabata yana da shekaru 67. A lokacin rayuwarsa, malamin…

CNPP a Kaduna ta yi tir da kiran AYCF na neman a ayyana dokar ta-baci a Zamfara

Ƙungiyar CNPP reshen Jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Mallam Mikailu Abubakar ta yi kakkausar suka tare da yin Alla-wadai da kiran da Ƙungiyar Tuntuba ta Matasan Arewa (AYCF) ta yi na a ƙaƙaba dokar ta-baci a Jihar Zamfara. Ƙungiyar ta…

Gwamna Lawal Ya Karbi Baƙuncin Jami’an Hukumar NSCDC 10 ‘Yan Asalin Zamfara Da Suka Samu Ƙarin Girma

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya karbi baƙuncin jami’an hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) su goma ‘yan asalin jihar bayan samun ƙarin girma. Jami’an da aka yi wa ƙarin girma sun samu jagorancin kwamandan NSCDC na shiyya 2, ACG…

Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ware Naira Bilyan 15 Don Tunkarar Ambaliyar Ruwa

Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ware tsabar kuɗi har Naira Biliyan 15 ga Hukumar bayar da agajin gaggawa ta tarayya (NEMA) don shirye-shiryen tunkarar ambaliyar ruwan da ka-iya faruwa a…

Fadar shugaban ƙasa ga ƴan adawa: Ku daina ɗora mana lefin gazawarku

Fadar Shugaban Kasa ta yi kira ga yan adawa da su daina ɗora laifin gazawar su ga Gwamnati, ta kuma bayyana cewa demokaradiyya na nan daram a Najeriya, babu wani yunƙuri na hana ‘yancin siyasa ko wani yunƙuri na kafa…