ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Year: 2025

Na Karɓi Mulki Lokacin Da Jihar Zamfara Ke Fama Da Matsaloli Ta Kowace Fuska– Gwamna Lawal

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya bayyana cewa, lokacin da ya karɓi mulki daga tsohon gwamna Bello Matawalle, jihar Zamfara tana cikin matsaloli ta kowace fuska. Ya bayyana cewa rashin tsaro ya yi katutu, tsarin ilimi…

ƘUNGIYAR KASUWANCI TA NIJERIYA DA AMURKA TA KARRAMA GWAMNA LAWAL BISA AYYUKAN INGANTA RAYUWAR AL’UMMA A ZAMFARA

Ƙungiyar Kasuwanci ta Nijeriya da Amurka (NACC) ta karrama Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal da babbar lambar yabo ta jagoranci da hidimar al’umma. A ranar Asabar ne ƙungiyar ta yi bikin cika shekaru 65 da kafuwa, tare da ƙaddamar da…

Ministan Yaɗa Labarai Ya Gargaɗi Jami’an Gwamnati Kan Rashin Ilimin Kafofin Watsa Labarai

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi gargaɗin cewa jami’an gwamnati da ba su da ilimi kan kafofin watsa labarai suna cikin haɗarin faɗawa tarkon yarda da labaran ƙarya. Mataimaki na musamman ga Ministan kan…

Ministan Yaɗa Labarai ya nuna wa masu zuba jari na Faransa irin sauye-sauyen tattalin arzikin Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jawo hankalin masu zuba jari daga ƙasar Faransa, inda ya jaddada masu irin sauye-sauyen tattalin arziki masu ƙayatarwa, damar kasuwanci mai faɗi da yanayin da ya dace da masu…

Idris Ya Musanta Rahoton Wai Ya Ce A Yi Watsi Da Damuwar Gwamna Zulum Kan Tsaro

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ƙaryata wani rahoto da ke cewa wai ya ce a yi watsi da damuwar da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi kan batun tsaro. A wata sanarwa da…

Gwamnatin Tarayya ta fara sabunta kayan aikin gidajen watsa labarai, cewar Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta fara zuba jari wajen samar da sababbin fasahohi da na’urorin zamani domin ƙarfafa ayyukan kafafen yaɗa labarai na gwamnati. Ya bayyana hakan ne a…

Sama da mutane 3,300 suka rasu sakamakon girgizar kasa a Myanmar

Yawan mutanen da suka rasu sakamakon girgizar kasa a Myanmar ya wuce 3,300, kamar yadda kafar watsa labarun kasar ta bayyana a ranar Asabar, a yayin da babban mai kula da taimakon jin kai na majalisar dinkin duniya ya sabunta…

Dk. Idris Abdul’aziz ya rasu, ya yi wasicin kar a je makabartarsa da takalmi, kuma ban da daukar hoto

Shahararren malamin nan mai yawon jawo cece-kuce, Dk. Idris Abdul’aziz, ya rasu bayan fama da rashin lafiyar da ba a bayyana ba a jiya Alhamis 3 ga Afrilu, 2025 da dare. Shafin sada zumunta na Facebook na masallacin sa, Dutsen…

Rundunar sojojin Yemen ta sake harbo jirgin yakin Amurka mara matuki na US MQ-9

Rundunar sojin kasar Yemen ta bayyana cewa ta sake harbo jirgin yaki mara matuki na US MQ-9, kwanaki uku bayan harbo na farko a makon da ya gabata, a matsayin wani bangare na goyon bayan raunana Falasdinawa da kuma hare-haren…

Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai yi zaman gaggawa kan yankunan Falasdinawa

Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai yi zaman gaggawa a yammacin ranar Alhamis domin tattaunawa kan halin da ake ciki a Gaza da kuma Yamma da gabar kogin Jordan biyo bayan bukatar hakan daga kasar Aljeriya. Kamar yadda kafar…