Gwamnatin Tarayya Ta Tura Manyan Motocin Yaki Guda Shida Don Yaki da Ƙalubalen Tsaro a Jihar Kebbi

A wani mataki na karfafa tsaro da dakile ayyukan ‘yan bindiga a jihar Kebbi, Gwamnatin Tarayya ta tura manyan motocin yaƙi da aka fi sani da Armoured Personnel Carriers (APCs) guda shida zuwa jihar domin yaki da ayyukan ta’addanci. Wannan na daga cikin matakan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke dauka wajen fuskantar matsalolin tsaro a sassan kasar nan.

Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ne ya bayyana hakan yayin da yake duba motocin a harabar Gidan Gwamnati da ke Birnin Kebbi, tare da nuna godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da manyan hafsoshin tsaro na kasa.

Gwamnan ya ce Kebbi, musamman yankin kudancin jihar, na fuskantar hare-hare daga ‘yan bindiga da ke shiga daga jihohin Zamfara da Neja, suna kai farmaki sannan su gudu zuwa maboyarsu. Ya ce tura wadannan motocin zai taimaka wajen hana su sake kai hare-hare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

“Ina mika godiya ta ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, da Babban Hafsan Sojojin Kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, da sauran shugabannin hukumomin tsaro bisa wannan matakin gaggawa da suka dauka domin kare rayukan al’ummar jihar Kebbi,” in ji Gwamna Idris.

Gwamnan ya kara da cewa gwamnati na kara ba da goyon baya ga jami’an tsaro da kuma iyalan jaruman da suka rasa rayukansu a fafatawa da ‘yan bindiga, domin tabbatar da cewa an samu zaman lafiya mai dorewa a jihar.

A nasa bangaren, Kwamandan Rundunar 223 Light Tank Battalion da ke Zuru, Laftanar Kanar M. S. Saleh, ya nuna wa gwamnan kayan yaki da aka turo, tare da gode wa gwamnatin tarayya da ta jihar bisa hadin kai da tallafi da suke bayarwa domin ganin an shawo kan matsalar tsaro a jihar.

Ya bukaci al’umma da su ci gaba da hada kai da jami’an tsaro ta hanyar bayar da bayanan sirri da za su taimaka wajen gano maboyar ‘yan ta’adda da kuma hana su samun kafa a cikin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *