NELFUND: Gwamnatin Tarayya ta kashe sama da Naira biliyan 2 don biyan kudin karatun ɗalibai 20,919 a Arewa maso Yamma

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta kashe sama da Naira biliyan 2.08 domin tallafa wa ɗaliban manyan makarantu a shiyyar Arewa maso Yamma ta hanyar shirin Nigerian Education Loan Fund (NELFUND).

Daraktan Hukumar Wayar da Kai ta Kasa (NOA) a Jihar Katsina, Alhaji Mukhtar Lawal-Tsagem, ne ya bayyana hakan a Katsina, yayin wani taron wayar da kai da Ma’aikatar Ƙididdiga da Wayar da Kai ta shirya a ranar Talata.

Ya ce an raba kuɗin ga dalibai 20,919 daga jihohin Arewa maso Yamma domin biyan kuɗin makaranta da kuma tallafawa karatunsu.

Lawal-Tsagem ya kara da cewa, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta bada tallafi ga Manoman alkama a kananan hukumomi 12 na Jihar Kebbi a karkashin shirin ta na NAGAP. A Jihar Kaduna kuma manoman citta sun samu tallafin Naira biliyan 1.6.

Ya kara da cewa, a Jihar Kebbi, an kaddamar da shirin samar da ruwa a Yawuri mai darajar Naira biliyan 2.

Shirin NELFUND na bayar da rancen bashi mara ruwa ga ɗaliban manyan makarantu, wanda zai taimaka musu wajen biyan kudin makaranta da sauran bukatun karatu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *