Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da wani shirin horas da fiye da matasa 260,000 a fannonin sana’o’in dogaro da kai a fadin kasar nan, karkashin shirin Technical and Vocational Education and Training (TVET).
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a yau Alhamis yayin da yake duba wasu cibiyoyin gudanar da shirin a birnin Abuja.
A cewar Ministan, gwamnati na da burin horas da sama da matasa 900,000 a matakai daban-daban na wannan shiri, domin bai wa matasa damar samun kwarewa da za ta basu ikon dogaro da kansu tare da inganta tattalin arzikin kasa.
“Muna da cibiyoyi sama da 2,600 a fadin kasar nan. Wannan mataki na farko zai kunshi mutum 260,000, kuma mataki na gaba zai kara kusantar da mu burin horas da mutum 960,000” in ji shi.
Dr. Alausa ya kara da cewa shirin yana gudana a dukkan jihohin kasar nan da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja. Ya kuma tabbatar wa mahalarta cewa za su samu kudin tallafi da kayan farawa bayan kammala horo, domin su kafa kananan sana’o’insu.
Ministan ya bayyana shirin a matsayin wani bangare na hangen nesa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen farfado da ilimin sana’a da kuma karfafa tsarin TVET a matsayin ginshikin ilimin kasar.
Ya ce Shugaban Kasa ya amince da ware kashi 5% na kasafin TETFund domin tallafa wa ci gaban shirin TVET a duk shekara, abin da ya bayyana a matsayin matakin dorewar shirin.
An kaddamar da shirin TVET tun a watan Yuni, a matsayin wani bangare na yunkurin gwamnatin Tinubu na karfafa ilimin sana’o’i da habaka damar aikin yi ga matasa.
Shirin, wanda zai dauki lokaci tsakanin watanni shida zuwa goma sha biyu bisa ga irin sana’ar, ya kunshi fannonin kiwon dabbobi, kiwon kifi, ƙera tukwane na zamani, da sauran sana’o’in hannu.
A halin yanzu, ana gudanar da horon ne a cikin cibiyoyi sama da 2,600 a fadin Najeriya.
