NFTD ta jinjina wa Yakubu, Babban Daraktan Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Tarayya

Ashafa Murnai Barkiya

Ƙungiyar NFTD, mai rajin jaddada bin ƙa’ida da bayyana yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati, ta jinjina tare da nuna yabo ga Babban Daraktan Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Tarayya, Tanimu Yakubu, dangane da yadda ya fito da tsarin fayyace yadda ake aiwatar da ayyukan kasafin kuɗi a fili.

NFTD ta kuma yaba ƙoƙarin Yakubu bisa yadda yake sa-ido sosai wajen yadda ake aiwatar da kasafin, tare da auna shi bisa gwargwadon ma’aunin da ya dace.

Cikin wata sanarwar da Babban Kodineta na Ƙasa na ƙungiyar, mai suna Joshua Oyenuga ya fitar a ranar Lahadi, mai ɗauke da sa hannun sa, ƙungiyar ta bayyana cewa, rahoton da Yakubu ya fitar kan yadda aka aiwatar da Kasafin 2024, “wani sabon babi ne sahihi a ƙasar nan kan yadda ake sa-ido wajen kashe kuɗaɗe a ɓangarorin ayyukan kasafi.”

NFTD ta ci gaba da cewa report ɗin na Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Tarayya ya nuna yadda Ma’aikatun Gwamnati, Hukumomi, Cibiyoyi da Rassan Ma’aikatu suka yi amfani da kashi 81 bisa 100 na kuɗaɗen da aka sakar masu domin aiwatar da manyan ayyukan rasa ƙasa.

Ya ce hakan na nuni da yadda Yakubu da ofishin sa ke nuna ƙwarewar iya aiki tare kuma da kishin fito da ƙa’idar aikin kashe kuɗaɗen shigar gwamnati a fili wajen fayyace komai dalla-dalla, ƙeƙe-da-ƙeƙe, ba tare da nuƙu-nuƙu ba.

“A ƙarƙashin Tanimu Yakubu, Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Tarayya ya sake fasalin yadda ake sa-ido kan kuɗaɗen gwamnati.

“Domin a yanzu abin da muke gani akwai daidaito tsakanin kuɗaɗen kasafin kuɗaɗen da gwamnati ke fitarwa, yawan ayyukan da ake yi da kuɗaɗen da kuma sakamakon da al’umma ‘yan Nijeriya za su iya bin-diddigin tabbatarwa da idon su.” Inji NFTD.

Sannan kuma an bayyana kasafin 2024 cewa yana ɗaya daga cikin kasafin da aka fi tsetstsefewa, aka aiwatar da shi filla-filla ba tare da ƙumbiya-ƙumbiya ko rufa-rufa ba a cikin shekarun nan.

“Musamman yadda Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Tarayya ɗin ke fitar da rahotanni bayan kowane watanni ukun cikin shekara, wato sau huɗu kenan a cikin shekara. Kuma ake bugawa tare da wallafa rahotannin a fili kowa na gani.”

Sanarwar ta ce yadda Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Tarayya a ƙarƙashin Yakubu ke baje bayanan kasafin kuɗaɗe a fili, hakan ya ƙara cusa wa jama’a samun yaƙini da gamsuwa kan yadda ake tafiyar da gwamnati a fannin kashe kuɗaɗen al’umma. Kuma hakan yana ƙara wa kasafin ƙima da darajar gamsuwa da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *