Jimamin Rasuwar Janar Abdullahi Mohammed, GCFR, Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa

Daga Tanimu Yakubu

Rasuwar Janar Abdullahi Mohammed, GCFR, fss, psc, mni, mni ta kawo ƙarshen wani muhimmin tarihin sadaukarwa ga aikin gwamnati da kuma fannin tsaron ƙasa. Marigayi Janar Abdullahi gwarzo ne da ya nuna tsantsar kishi, sadaukarwa, ɗa’a da biyayya ga ƙasa. Hakan ne ya sa ya fita daban, yadda ba kasafai ake samun irin sa ba. Ya kasance cikin irin gwarzayen manyan sojojin da ke faɗa-a-ji da suke shuɗe. Haziƙi ne mai cikakar baiwar ƙwarewar aikin soja da matuƙar gogewa da aikin gwamnati, bisa taka-tsantsan da kuma bin ƙa’ida.

Farkon kusanci na da shi, lokacin da ina Shugaban Federal Mortgage Bank (FMBN), daidai lokacin da wasu dalilai suka sa za ni gana tare da shugaban ƙasa na wancan lokaci, Shugaba Olusegun Obasanjo, GCF, na je ne tare da ministan da nake ƙarƙashin sa.

Na yi jajircewa tsayin-daka domin kare darajar bankin, tare da ƙin yarda na sallama wa matsin-labbar da wasu daga sama ke yi min. To a cikin wannan yanayi ne a irin wannan zama da manya na samu tubarrakin ganin yadda ake gudanar da aikin gwamnatin tarayya bisa kyakkyawan tsari a hannun su Janar Abdullahi Mohammed, wanda a lokacin shi ne Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, sai kuma Alhaji Yayale Ahmed, CFR yana Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, sai marigayi Joseph Ekaette, CFR yana Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Zan yi wa waɗannan nagartattun manyan ma’aikatan gwamnati kyakkyawar shaidar cewa duk da rashin samun daidaiton matsaya da fahimta iri ɗaya da na riƙa samu da su, an riƙa tattauna batutuwa m ne bisa adalci ga juna. Ba su taɓa nuna ƙoƙarin tirsasa na bi ta su fahimtar ba, saboda ina ƙasa da su.

Kuma idan ana tattauna wasu muhimman batutuwa ana bijiro da mafita, ba a taɓa cewa na tashi na fita ba. Duk kuwa da cewa a lokacin muƙaman su ya wuce matsayi na fintinkau. Wannan kusanci da na yi da su kyakkyawar shaida ce da ta sa na tabbatar da irin sauƙin kai da kamilin mutum mai jajircewa wajen ganin an aiwatar da sha’anin gudanar da aikin gwamnati bisa cancanta da ƙwarewa yake da shi.

Gagarimar gudummawar da Janar Abdullahi Mohammed ya bayar ta yi tasiri tun daga tirka-tirkar zamanin mulkin sojoji har zuwa bada mulki ga farar hula. A matsayin sa na haziƙin matashin jami’in soja zuwa babban jami’in soja a zamanin mulkin Murtala da na Obasanjo, ya bada muhimmiyar gudummawa wajen sake cusa ɗa’a da sauya fasalin tafiyar da tsarin aikin gwamnatin tarayya, bayan yaƙin basasa. Yana sahun gaba wajen tsara harkokin tsaron ƙasa, inda har aka kai ga kafa Hukumar Tsaro ta ‘National Security Organization, wato NSO da sauran hukumomin leƙen siri da suka biyo bayan NSO ɗin.

Naɗa shi da aka yi muƙamin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa lokacin Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo (1979-2007) da kuma ci gaba da riƙe muƙamin da ya yi a zamanin Shugaban Ƙasa Umaru Musa Yar’Adua, GCFR, wata kyakkyawar shaida ce da ta nuna irin yadda gwamnatocin suka amince da shi bisa ɗabi’ar sa ta gaskiya da riƙon amana.

Ƙalilan ne a cikin mutane a samu mai irin nagartar Janar Mohammed, wanda ya fahimci ƙabli da ba’adin aikin gwamnatin da kuma aikin soja. Marigayi Janar Abdullahi Mohammed ya zama abin buga misali da irin cancanta, gogewa, ɗa’a da kuma kaifin tunanin sa. Waɗannan sune manyan sabubba masu nuna nagartar aiki ga Fadar Shugaban Ƙasa a lokacin da ake kan ganiyar ɗora dimokuraɗiyya bisa kyakkyawar turba.

Lokacin da na samu damar zama Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa a zamanin mulkin Shugaban Ƙasa Yar’adua, na fahimci irin zurfin martabar faɗa-a-ji da Janar Abdullahi Mohammed ke da shi. Ba wai nuna isa ya riƙa yi ba, ya yi tasiri ne wajen bayar da shawara da nasiha a tsanake, kazar-kazar wajen gudanar da aiki bisa tsari, da kuma fahimtar yadda shugabanci yake a Nijeriya. Kai da ganin sa ka ga wanda ya fahimci tsarin aikin gwamnatin farar hula da na gwamnatin mulkin soja: jajirtacce ne da ke aiki ba don ganin-ido ba, kuma ka ga jagoran da ba ya nuna isa ko fankama.

Abin da ma ya fi ɗaukar min hankali da marigayi, baya ga ƙwaƙwalwa da haziƙancin sa da iya gudanar da aiki, shi ne yadda bai taɓa fitowa yana yayata ɗabi’ar ninanci kan wata bajintar da ya taɓa yi a baya ba. Duk da irin rawar da ya taka wajen shirya juyin mulkin da Murtala Ramat Mohammed ya zama Shugaban Ƙasa a 1975, Janar Abdullahi bai taɓa fitowa ko sau ɗaya ya yi bugun-gaba ba. Shi dai ka bar shi ga jajircewa ga yin aiki tuƙuru ga ƙasar sa.

Haƙiƙa Nijeriya ta yi babban rashin ɗaya daga cikin masu kishi, kuma ɗaya daga cikin gadojin da suka haɗa mulkin soja da gwamnatin dimokraɗiyya.

Yayin da muke jimamin rashin sa, muna kuma tutiya da irin gagarimar sadaukarwar da ya yi wa ƙasar sa: Ya yi rayuwa mai sadaukarwa ga bin doka da oda, cusa ɗa’a, biyayya da kuma ɗabbaƙa mulkin dimokraɗiyya a Nijeriya.

Allah Ya gafarta masa kurakuran sa, Ya amshi kyakkyawan aikin da ya yi, Ya saka masa da Aljanna Firdausi. Allah Ya bai wa iyalan sa, abokan aikin da sojoji da ƙasar nan da ya yi wa aiki tuƙuru haƙuri.

*Tanimu Yakubu
Tsohon Mashawarcin Shugaban Ƙasa Tattalin Arziki kuma Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa na Tarayyar Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *