Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, murnar cika shekaru 70 da haihuwa.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Litinin a Abuja, Shugaba Tinubu ya yaba da rawar da Shekarau ya taka a fagen hidimar jama’a da kuma siyasa a Najeriya.
Shugaba Tinubu ya bayyana Shekarau a matsayin ƙwararren jami’in gwamnati wanda ya fara aiki a matsayin malami, kafin daga baya ya zama babban sakatare a ma’aikatar jihar Kano, sannan daga bisani ya shiga siyasa a farkon shekarun 2000.
Ya kuma bayyana nasarar da Shekarau ya samu a zaɓen gwamnan Jihar Kano a shekarar 2003, tare da irin tsarin mulkinsa na kula da walwalar jama’a a tsawon wa’adin mulkinsa biyu.
Bayan ya kammala mulkinsa, Shekarau ya yi aiki a matsayin Ministan Ilimi tsakanin 2014 da 2015, sannan daga baya aka zaɓe shi Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya daga 2019 zuwa 2023.
Shugaba Tinubu ya gode wa Shekarau bisa gudunmawar da ya bayar ga ci gaban ƙasa a matsayin malami, jami’in gwamnati, da kuma ɗan siyasa mai kishin ƙasa.
Ya yi addu’a ga Allah Ya ba shi lafiya da ƙarfi domin ci gaba da hidima ga al’umma da ƙasarsa baki ɗaya.
