Gwamnati Ta Roƙi ‘Yan Nijeriya Su Kwantar da Hankali Kan Rikicin Diflomasiyya da Amurka

Gwamnatin Tarayya ta buƙaci ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankalin su dangane da rikicin diflomasiyya da ake ciki tsakanin Nijeriya da Amurka.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya yi wannan kiran a garin Dutse, Jihar Jigawa, yayin ziyarar ban-girma da ya kai wa Gwamnan Jihar, Malam Umar A. Namadi.

A cewar sa, “Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana da duk abin da ake buƙata don kare Nijeriya daga masu neman tayar da hankali, tare da gyara duk wata ɓaraka da ta taso tsakanin ƙasar mu da abokan hulɗar mu na ƙasashen waje. Don haka ina roƙon ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankalin su.”

Idris ya je Jihar Jigawa ne domin halartar Taron Matasa na Arewa-maso-yamma na shekarar 2025 da kuma gabatar da nasarorin da Shugaban Ƙasa Tinubu ya cimma bayan shekaru biyu a kan mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *