SHIRIN BUNƘASA TATTALIN ARZIKI: CBN da Gwamnatin Tarayya sun ƙaddamar da Shirin Daƙile Tsadar Rayuwa da Hauhawar Farashi (DGAS)

Ashafa Murnai Barkiya

Babban Bankin Nijeriya (CBN) tare da Gwamnatin Tarayya sun ƙaddamar da Shirin Daƙile Tsadar Rayuwa da Hauhawar Farashi, domin zaburar da harkokin tattalin arziki bunƙasa.

Shirin mai suna Dis-inflation and Growth Acceleration Strategy (DGAS), an ƙaddamar da shi ne domin hana malejin tsadar rayuwa da na farashin kayayyaki cillawa sama zuwa kashi 10 abin da ya yi sama. Wato ana so kada ma ya riƙa haura kashi 9 zuwa sama.

Kakakin Yaɗa Labarai na Shugaban Ƙasa, Olusegun Dada ne ya sanar da haka a shafin sa na X a ranar Laraba.

Ya ƙara da cewa shirin zai haɓɓaka samun kuɗaɗen shiga ga magidanta, ta yadda samun zai ruɓanya nan da shekaru biyu.

Ya ce shirin zai maida ƙarfi wajen bunƙasa tattalin arzikin cikin gida (GSP) sama da kashi 7 bisa 100, ya sauko da hauhawar farashi da tsadar rayuwa zuwa ƙasa da kashi 10 bisa 100. Sannan zai sassauta fatara da talauci ta hanyar daudaitaccen tsare-tsaren harkokin kuɗaɗe mai fa’ida.

Cikin Satumba 2025 ne Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki sun yi ƙasa da kashi 18.02 bisa 100 cikin watan na Satumba 2025.

Wannan sauƙin farashin kayayyaki musamman na abinci, rabon da a samu kamar sa dai tun cikin watan Juni 2022, inda ya yi sauƙi zuwa kashi 18 bisa 100, kamar yadda rahoton bayanan CBN ya tabbatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *