Jami’ar Tarayya ta Dutse Ta Karɓi Naira Miliyan 867 Don Tallafin Kuɗin Dalibai 7738 Daga NELFUND

Jami’ar Tarayya ta Dutse (FUD), dake Jihar Jigawa, ta bayyana cewa ta karɓi jimillar N867,381,000 daga Hukumar Tallafin Kuɗin Karatu ta Ƙasa (NELFUND) domin biyan kuɗin karatu na dalibanta.

A cewar wata sanarwa da Babban Akanta (Bursar) na jami’ar, Malam Hassan Balarabe, ya fitar a ranar 10 ga watan Nuwamba, an bayyana cewa kuɗin sun haɗa da N844,273,000 da aka ware wa ɗalibai 7,546, da kuma N23,108,000 ga dalibai 192.

Balarabe ya ce jimillar kuɗin da aka samu ya kai N867,381,000, wanda aka riga aka tura don biyan kuɗin waɗannan dalibai a ƙarƙashin tsarin tallafin da gwamnatin tarayya ta ƙaddamar.

Ya ƙara da cewa jami’ar na godiya ga gwamnatin tarayya da hukumar NELFUND bisa wannan taimako da zai rage wa ɗalibai da iyayensu nauyin kuɗin karatu, tare da ƙarfafa ci gaba da karatu cikin kwanciyar hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *