ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Labarai

GARGAƊI DAGA CBN: A Yi Guji Yin Hulɗa Da ‘Zuldal Microfinance Bank’, Ba Shi Da Lasisi

Ashafa Murnai Barkiya

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya gargaɗi jama’a cewa kada su kuskura su yi mu’amala da wani banki mai suna Zuldal Microfinance Bank’, domin ba shi da lasisin iznin yin hadahadar kuɗaɗe daga CBN.

Cikin wata sanarwar da CBN ya fitar a ranar 19 ga Nuwamba, 2025, mai ɗauke da sa-hannun Daraktar Riƙo ta Sashen Hulɗa da Jama’a, Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Hajiya Hakama Sidi Ali, ta ce bankin ba shi da lasisin kafa ofisoshin rassan sa a Legas, Abuja, Kano da Kaduna, kamar yadda aka sanar wa CBN an kafa rassan.

“An ja hankalin Babban Bankin Nijeriya (CBN) dangane da wani bankin da aka kafa mai suna ‘Zuldal Microfinance Bank’. Bankin ba shi da lasisin iznin kafuwa, kuma an ce har ya buɗe rassa a Legas, Abuja, Kano da Kaduna.

“To jama’a su yi kaffa-kaffa da shi, domin ba a ba shi izni daga CBN ba, kamar yadda doka ta gindaya cewa sai da lasisin iznin CBN ake kafa banki.

“Sashe na 2(1) na Dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Hadahadar Kuɗaɗe (BOFIA) ta shekarar 2020, ta ce kada wani ko wasu gungun jama’a su kafa banki ba tare da lasisin izni daga CBN ba.” Inji Hajiya Hakama.”

A ƙarshe ta jaddada cewa jama’a su yi hattara da wannan banki, kuma CBN zai ci gaba da aikin sa na kare jama’a daga afkawa hannun ‘yan damfara, masu kafa cibiyoyin hadahadar kuɗaɗe da sauran mu’amalolin kuɗi ba tare da izni ba.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *