Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce babu wata babbar damuwa da ke tasiri a zuciyar sa fiye da matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a Nijeriya, musamman tashin hankalin da ya addabi sassa da dama a Arewa.
Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Asabar a Kaduna, yayin bikin cikar Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (Arewa Consultative Forum, ACF) shekaru 25 da kuma ƙaddamar da Asusun Tallafin ta.
Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Tajudeen Abbas, shi ne ya wakilci Tinubu a wajen taron.
Shugaban Ƙasa ya bayyana matsalar tsaro a matsayin barazana mafi tsanani da ƙasar nan take fuskanta, yana mai jaddada cewa Nijeriya ba za ta iya komawa kan turbar farfaɗowar tattalin arziki ko zaman lafiyar al’umma ba muddin ba a dawo da zaman lafiya ba.
“Babu abin da ke damu na sosai fiye da matsalar tsaro da ke addabar Nijeriya, musamman Arewacin Nijeriya,” inji shugaban.
Ya ƙara da cewa, “Ba za mu ci gaba ba idan wani ɓangare na jikin ƙasa ya tsaya cik.”
Ya ce gwamnatin sa ta gaji yanayin tsaro mai rikitarwa ne wanda ya haɗa daga ta’addanci zuwa ta’addancin ’yan fashi da garkuwa da mutane, amma tana fuskantar matsalar da gaggawa, da jajircewa da kuma bin sababbin tsare-tsaren gyara.
Tinubu ya ce Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar kawar da ƙungiyoyin ’yan ta’adda da ’yan bindiga da ke addabar Arewa tare da dawo da ƙarfin tattalin arzikin yankin da rikice-rikice suka daɗe suna durƙusarwa.
Ya bayyana cewa gina amana tsakanin al’umma, ƙarfafa haɗin kai da dawo da tsaro matakai ne da dole a ɗauka domin hana rikicin ya ƙara lalacewa, musamman a ɓangaren ilimi da noma.
Duk da ƙalubalen da ake fuskanta, Tinubu ya nuna ƙwarin gwiwa game da makomar tattalin arzikin Arewa.
Ya ce yana fatan ganin lokacin da manyan motoci masu ɗaukar ɗanyen man fetur za su fara fita daga Kolmani da sauran sababbin wuraren haƙar mai na Arewa, alamar sababbin damar masana’antu da ƙaruwar kuɗaɗen shiga.
Ya ƙara da cewa manyan ayyukan gine-gine, ciki har da babban titin Abuja–Kaduna–Kano, ana hanzarta aikin su domin kammala su don bunƙasa zirga-zirga, cinikayya da haɗe yankuna.
Tinubu ya ce dole Arewa ta fuskanci matsalolin ta da gaskiya, jarumta da jagoranci mai haɗe kai.
“Mun gaza samun ranar da muke yin barci cikin kwanciyar hankali alhali miliyoyi suna kwanciya da yunwa, ranar da tsoro ya zama abokin tafiya na dindindin ga matafiya,” inji shi.
Ya nuna cewa shekaru da dama na tangal-tangal sun raunana haɗin kai, amma bambance-bambancen jama’ar da aka gani a bikin cikar ACF shekaru 25 alama ce ta sabuwar aniyar ƙin rarrabuwa da dawo da zumunci.
Shugaban ya yaba wa ACF bisa kasancewa “lamirin Arewacin Nijeriya” a tsawon shekaru 25 da suka gabata.
Ya ce zagayowar bikin murnar shekarun ta nuna shekaru na jarumtaka, kare gaskiya da hidimta wa al’umma wajen kare mutunci, adalci da daidaito ga miliyoyin ’yan Arewa.
Tinubu ya yi kira ga shugabannin siyasa, gargajiya, al’umma da addini da su sake dagewa wajen kiyaye manufofin da suka sa aka kafa ACF, yana mai jaddada cewa zaman lafiyar Arewa muhimmin ginshiƙi ne ga zaman lafiya da cigaban Nijeriya baki ɗaya.





