Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na kare rayuka da dawo da tsaro a faɗin ƙasar nan, yayin da Nijeriya da Amurka suka ƙarfafa haɗin gwiwa kan tsaro, ’yancin addini da kare fararen hula.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja, yayin da yake yi wa manema labarai bayani bayan taron haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da Amurka, wanda aka gudanar a Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA), Malam Nuhu Ribaɗu.
Taron ya mayar da hankali ne kan batun sanya Nijeriya a matsayin “Ƙasar da ke da Damuwa ta Musamman”.
A cewar Ministan, wannan zama shi ne karo na uku da aka yi irin wannan ganawa tsakanin Nijeriya da manyan jami’an Amurka tun daga watan Nuwamba 2025, lamarin da ke nuna ƙarfi da ɗorewar dangantakar ƙasashen biyu.
Ya ce wannan haɗin gwiwar yana nuna matsaya ɗaya kan kare ’yancin addini, kare farar hula, da kuma dangantaka mai ma’ana wadda aka gina kan gaskiya da amana.
Malam Nuhu Ribadu da Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka kan Harkokin Siyasa, Allison Hooker, su ne suka jagoranci zaman taron.
Idris ya bayyana cewa haɗin gwiwar tsaro da Amurka ya haifar da nasarori na gaske ga tsarin tsaron Nijeriya.
Ya ce sojojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro suna aiki kafaɗa da kafaɗa da takwarorin su na Amurka ta hanyar musayar bayanan sirri da haɗin kai a ayyukan tsaro, wanda ya ƙarfafa manyan ayyuka kamar “Operation Haɗin Kai” a Arewa-maso-gabas da “Operation Fasan Yamma”.
Ministan ya ƙara da cewa Amurka ta yi alƙawarin gaggauta isar da sauran kayan aikin soja da Nijeriya ta saya cikin shekaru biyar da suka gabata, ciki har da jiragen leƙen asiri marasa matuƙa (drones), helkwaftoci, kayayyakin aiki, sassan gyaran makamai da na’urorin tallafi.
Dangane da matakan tsaro a cikin gida, Idris ya tunatar da cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci ta tsaro a wasu yankuna masu haɗari, inda ya ba da izinin ƙara haɗin gwiwar jami’an tsaro, tare da umurtar a ci gaba da tura dakarun tsaro zuwa wuraren da suka fi buƙatar kariya.
Ya ce an bai wa hukumomin tsaro umurni bayyananne na kare al’umma da kuma gaggauta ɗaukar mataki kan kowace barazana.
Ministan ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya tana ƙarfafa tsarin gargaɗin wuri-wuri tare da samar da kundin bayanai na ƙasa guda ɗaya da zai tattara sahihan alƙaluma kan mutuwar mutane da asarar rayuka sakamakon tashin hankali.
A cewar sa, hakan zai taimaka wajen yanke shawara mai inganci, tabbatar da bin ƙa’ida, da kuma inganta martanin tsaro.
Ya jaddada cewa tabbatar da adalci muhimmin ginshiƙi ne a dabarun tsaron gwamnati, yana mai cewa Ma’aikatar Shari’a, Hukumar DSS da Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya suna ci gaba da bincike da gurfanar da masu laifin ta’addanci domin tabbatar da adalci da hukunci.
Idris ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su ci gaba da haƙuri tare da ba gwamnati goyon baya yayin da ake aiwatar da gyare-gyaren tsaro, yana mai tabbatar da cewa dukkan matakan da ake ɗauka a yau suna da nufin tabbatar da ingantaccen tsaro ne a ƙasar nan.
Manyan jami’an gwamnati da suka halarci taron sun haɗa da Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya); Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede; Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Abubakar Atiku Bagudu; Ƙaramar Ministar Harkokin Kuɗi, Dakta Doris Uzoka-Anite; Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo; Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun; da Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam ta Nijeriya, Bashir Adewale Adeniyi.
Tawagar Amurka kuma ta haɗa da Mataimakiyar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka mai Kula da Harkokin Siyasa, Allison Hooker; Babban Jami’in Gudanarwa na Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya, Keith Heffern; Mataimakin Sakataren Harkokin Waje mai Kula da Dimokiraɗiyya, ’Yancin Ɗan’adam da Ƙwadago, Riley Barnes; Mataimakin Kwamandan AFRICOM, Laftanar-Janar John Brennan, tare da sauran manyan jami’ai daga Ma’aikatun Harkokin Waje da Tsaro na Amurka.
