Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa aikin bututun gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK) na ci gaba da gudana cikin nasara, a wani yunkuri na bunkasa masana’antu da habaka tattalin arzikin kasar.
Ministan Watsa Labarai da Wayar da Kai na Kasa, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a birnin Minna, jihar Neja, a yayin taron Gwamnonin Jam’iyyar APC da Kwamishinonin Watsa Labarai daga jihohin da APC ke mulki suka halarta.
Mohammed Idris ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na bai wa zuba jari a bangaren makamashi da ababen more rayuwa muhimmanci, domin ciyar da kasar gaba a matakin masana’antu. Ya ce aikin bututun AKK wanda ke da tsawon kilomita 614 daga Ajaokuta zuwa Kano, ta hanyar Abuja da Kaduna, ya riga ya ketare Kogin Neja, kuma yana tafiya tare da aikin bututun Obiafu–Obrikom–Oben (OB3), duka a wani bangare na shirin Bututun Iskar Gas da kewaye Najeriya na (Trans-Nigeria Pipeline Project)
Ministan ya kara da cewa, gwamnatin Tinubu ta kaddamar da wasu muhimman ayyuka kamar Masana’antar samar da Gas ta ANOH da AHL, wadanda za su samar da Gas da ya kai kimanin Cubic Feet miliyan 500 a kullum, karin kashi 25 cikin 100 na gas din da ake samarwa a cikin gida.
Haka kuma, ya ce an soma gina wasu kananan masana’antun sarrafa gas guda biyar a Ajaokuta, tare da janyo hannun jari na sama da dala miliyan 500 a bangaren CNG, domin samar da makamashi mai araha ga gidaje da masana’antu.