.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tana ƙara maida hankali wajen magance matsalolin tsaro a ƙasar nan domin tabbatar da tsaro da walwalar ’yan ƙasa.
Da yake magana a cikin wata hira da gidan talbijin na CNN ya yi da shi a London a daren Talata, Idris ya ƙaryata iƙirarin da wasu jami’an ƙasashen waje suke yi cewa wai ’yan ta’adda a Nijeriya suna kai hare-hare ne kan Kiristoci kawai.
Ya bayyana cewa irin waɗannan iƙirari ba su da tushe kuma ba su bayyana haƙiƙanin yanayin tsaron ƙasar nan, inda ya jaddada cewa ’yancin yin addini yana cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Ya ce: “Wasu daga cikin iƙirarin da wasu jami’an Amurka suka yi sun ta’allaƙa ne kan bayanai marasa inganci da kuma zato cewa yawancin waɗanda ake kai wa hare-hare Kiristoci ne. E, ana kai wa Kiristoci hari, amma waɗannan miyagun ba mabiya addini ɗaya kawai suke kai wa farmaki ba. Suna kai wa Kiristoci hari, suna kuma kai wa Musulmi hari, musamman a arewacin ƙasar.”
Idris ya ce masu yaɗa irin waɗannan labaran ƙaryar suna taimaka wa ’yan ta’addar ne, saboda manufar ’yan ta’adda ita ce su haddasa rikici tsakanin Musulmi da Kiristoci a ƙasar.
Ya ƙara da cewa Nijeriya ƙasa ce da ta yi yarda da bambancin addinai, don haka yaɗa labaran ƙarya na nuna rashin jituwa zai iya haifar da rarrabuwar kai.
Ya ce: “Kiran lamarin da cewa hare-haren kan Kiristoci ne kawai zai iya haifar da rarrabuwar kai a Nijeriya. Miyagun suna son a ɗauka kamar ana faɗa ne tsakanin Musulmi da Kiristoci. Mun shaida akwai hare-hare kan Kiristoci, kuma mun shaida akwai hare-hare kan Musulmi. Amma ba daidai ba ne a ce Nijeriya ƙasa ce da ba ta mutunta ’yancin addini, ko a ce ko’ina babu tsaro a Nijeriya. Nijeriya ƙasa ce mai aminci.”
Ministan ya amince cewa akwai matsalolin tsaro, amma kuma gwamnati tana ɗaukar matakai masu ƙarfi da tsari don magance su.
Ya bayyana cewa gwamnati ta ƙarfafa rundunonin tsaro tare da zuba jari a fannoni kamar noma da ayyukan jinƙai domin ƙarfafa zaman lafiya.
Ya ce: “Ko canje-canjen da aka yi na shugabannin hafsoshin tsaro kwanan nan duk don a ƙarfafa tsarin tsaron ƙasar ne, domin gwamnati ta iya magance kowace irin matsala a kan lokaci.”
