Ba Za Mu Taba Yin Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba, Inji Gwamnan Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya sake nanata matsayar sa kan sulhu da ‘yan ta’addar da ke kashe mutanen Zamfara ba dare ba rana, inda ya ce ba zai taba yin sulhu da su ba.

Gwamnan ya faɗa wa mutanen Zamfara cewa gwamnatinsa ba za ta taba yin sulhu da ‘yan bindiga ba, kuma za ta dage kan hakan.

Gwamnan, a ranar Alhamis, ya ziyarci wasu ƙauyuka da ’yan bindiga suka kai hari kwanan nan.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce ƙauyukan da aka ziyarta sun haɗa da Kagara, Dan Isa, da Kasuwar Daji, duk a Ƙaramar Hukumar Kauran Namoda.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnan ya kai ziyarar jaje ga al’ummar da abin ya shafa domin nuna jajircewar gwamnatinsa na tabbatar da tsaron su.

Gwamnan Zamfara ya jaddada wa mutanen garuruwan da ya ziyarta cewa gwamnatinsa ba za ta taba yin sulhu da miyagun ba.

“A jiya, na fara kai ziyarar jajantawa ga wasu daga cikin garuruwan da ‘yan bindiga suka farmaka a kwanakin nan. Tun da ba mu iya kammala wa ba jiya, shi ne na ci gaba da ziyarar a yau.

“Mun ziyarci garuruwa uku, inda na haɗu da mutanensu tare da jajanta masu kan abin da ya same su, na kuma yi masu magana cikin ƙarfafawa gwiwa.

“Tun lokacin da na hau mulki, na fito fili na faɗi matsaya ta, ba zan taba yin sulhu da waɗannan ‘yan ta’addar da ke kashe mutanemu ba, kuma ina nan kan bakata,” inji Gwamna Lawal.

Gwamna Dauda Lawal ya ci gaba da cewa, “Tsaro shi ne farko a fannonin da gwamnatina ta mayar da hankali a kansu, kuma mun sadaukar da komai domin ganin mun samar da tsaro.

“Burina shi ne na ga mun kare rayuka da dukiyoyin mutane na. Don haka ne ma gwamnatina ba za ta taba yin sulhu da ‘yan bindiga ba, saboda ba su da amana ko kaɗan.”

Gwamnan ya ce, a lokacin da yake shiga ƙauyukan, ya fahimci titunansu sun lalace don haka ya yi alƙawarin gyara masu domin su ma su samu sauƙin zirga-zirga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *