Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce an tsara babban titin ‘Trans-Sahara’ ne domin ƙarfafa haɗin gwiwar yankuna da buɗe damarmakin tattalin arziki.
Idris ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da ya jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya wajen duba aikin wanda ake ci gaba da yi mai tsawon kilomita 118 da ya tashi daga Kalaba zuwa Ibonyi.
Ya bayyana babban titin a matsayin ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnati da ake aiwatarwa a ƙarƙashin shirin Sabunta Fata na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Ministan ya bayyana cewa gina gada mai tsawon mita 700 da faɗin 12 a kan titin zai magance matsalar ambaliyar da ta daɗe tana addabar yankin Bakin Ruwa na N’dibe tare da dawo da damar zirga-zirga ga al’ummomin da abin ya shafa.
A cewar sa, yanzu ne karon farko da Jihar Ibonyi take samun manyan ayyuka masu yawa na Gwamnatin Tarayya a lokaci guda, wanda hakan alama ce ta jajircewar gwamnati wajen tabbatar da cigaba daidaitacce.
Haka kuma ya shawarci masu kwangilar aikin da su kiyaye inganci tare da hanzarta kammala aikin, yana tabbatar wa da jama’ar Nijeriya cewa gwamnati ta mayar da hankali kan ayyukan raya ƙasa da za su inganta rayuwa da hanyoyin samun abin dogaro a duk faɗin ƙasar nan.
Ana gina babban titin ‘Trans-Sahara’ ɗin ne ta hannun kamfanin Infouest Nigeria Limited a kan kuɗin da ya kai naira biliyan 445, kuma yana da shimfiɗar kankare mai ƙarfi, sannan ya haɗa Kalaba, Ibonyi, Binuwai, Nasarawa da Abuja.