Dantsoho Ya Nemi Ƙasashen Afrika Su Hada Kai Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwan Yankin

Daga Bello Hamza, Abuja

Shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA) kuma Shugaban Ƙungiyar Gudanar da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Yamma da Tsakiyar Afirka (PMAWCA), Dr. Abubakar Dantsoho, ya yi kira ga ƙasashe mambobinsu da su ƙarfafa haɗin gwiwa a yankin don amfana da albarkacin teku na Afirka da kuma haɓaka ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin Teku ta hanyar amfana da dimbin arzikin da ke cikin teku.

Da yake jawabi a taron Majalisar Dokoki ta 45 na shekara-shekara na PMAWCA a Pointe-Noire, Jamhuriyar Congo, Dantsoho ya ce, kamata ya yi, yankin ya yi amfani da arziki mai kamanceceniya da yake da shi, albarkatun ƙasa, da ɗimbin albarkatun teku wajen dunƙukewa wuri ɗaya domin samun ci gaba mai ɗorewa.

Dantsoho, wanda Babban Manaja na Harkokin gudanarwa, Ikechukwu Onyemekara ya wakilta, ya jaddada cewa ƙungiyar tana fifita sauyin yanayi da makamashi, da haɗin gwiwa wurin tattara bayanai, a matsayin ginshiƙai masu mahimmanci don sauya ayyukan tashar jiragen ruwa ta Afirka.

Dantsoho ya bayyana cewa, a taron Tashoshin Jiragen Ruwa na Duniya da aka yi a Kobe, Kasar Japan, shugabannin tashoshin jiragen ruwa na Afirka sun yi alƙawarin haɓaka ci gaban Tashoshin yankin ta hanyar tsarin dabaru uku – aiwatar da manufofi, sabunta haɗin gwiwa, da sauƙaƙe ciniki, wanda wannan shi ne abin da NPA ta ƙuduri aniyar aiwatarwa.

Shugaban na PMAWCA ya kuma yaba wa gwamnati da mutanen Jamhuriyar Congo saboda ɗaukar nauyin taron kuma ya yaba wa sakatariyar ƙungiyar bisa jajircewa wurin tabbatar da dandamalin tattaunawar tsakanin yankunan da kuma yadda ake samar da sabbin tsare-tsare a shugabancin kungiyar mai kula da teku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *