Gwamnatin Tarayya da Amurka sun amince su haɗa kai don inganta ’yancin addini da ƙarfafa tsaro a Nijeriya

Gwamnatocin Tarayya da ta Amurka sun cimma matsaya kan cewa daga yanzu za su haɗa gwiwa don inganta ’yancin yin addini tare da ƙarfafa tsaro a duk faɗin Nijeriya.

Yarjejeniyar ta biyo bayan taron farko na Guruf ɗin Aikin Haɗin Gwiwa na Amurka da Nijeriya wanda aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis, 22 ga Janairu, 2026.

An kafa wannan Guruf ɗin Aiki ne sakamakon sanya Nijeriya a matsayin Ƙasa Mai Bada Matukar Damuwa (wato “Country of Particular Concern”) da Shugaban Amurka Donald J. Trump ya yi a ƙarƙashin Dokar ’Yancin Yin Addini ta Ƙasa da Ƙasa (International Religious Freedom Act).

Ta hanyar haɗin gwiwa ta ƙut-da-ƙut, manufofin Guruf ɗin Aikin su ne rage tashin hankali da ake yi wa ƙungiyoyi masu rauni a Nijeriya, musamman Kiristoci, da kuma samar da yanayi mai kyau da zai ba dukkan ’yan Nijeriya damar yin addinin su cikin ’yanci ba tare da cikas daga ’yan ta’adda, ’yan a-ware, ’yan fashi da makami, da ƙungiyoyin ’yan bindiga ba, ko kuma duk waɗanda ke son cutar da fararen hula ba tare da la’akari da addinin su ba.

A taron na Abuja, Mashawarci ga Shugaban Ƙasa kan Tsaron Ƙasa, Malam Nuhu Ribaɗu, shi ne ya jagoranci tawagar Nijeriya wadda ta ƙunshi Ma’aikatun Gwamnati da hukumomi guda 10, yayin da Ƙaramar Sakataren Harkokin Waje ta Amurka, Allison Hooker, ta jagoranci tawagar Amurka wadda ta ƙunshi hukumomin tarayyar ƙasar guda takwas.

A takardar bayan taron wadda aka raba wa manema labarai a ranar Alhamis, an bayyana cewa tattaunawar dabaru a zaman da aka yi sun mayar da hankali ne kan fannoni da dama na batutuwa da ƙalubale inda haɗin gwiwar Amurka da Nijeriya zai inganta ’yancin yin addini tare da ƙarfafa tsaro a faɗin ƙasar nan.

Ɓangarorin biyu sun yi la’akari da cewa akwai fa daɗaɗɗiyar alaƙa a tsakanin ƙasashen biyu, wadda ta ginu bisa ƙimomin haɗin kai na al’ummomi masu bambancin ra’ayi, girmama doka da oda, da mutunta ikon ƙasa.

Ɓangaren Amurka sun yi maraba da bayanin sake daidaita albarkatun Nijeriya domin magance rashin tsaro, musamman a jihohin Arewa-ta-Tsakiya. Gwamnatocin biyu sun sake jaddada ƙudiri mai ƙarfi da ba ya sassauci na kare ƙa’idojin ’yancin yin addini, tare da buƙatar ɗaukar matakai na haɗin gwiwa, masu ɗorewa da aiki tuƙuru, domin haɓakawa da kare ’yancin faɗar albarkacin baki, taron lumana, da ’yancin addini ko aƙida ga kowa, daidai da Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya.

Mahartan taron sun kuma jaddada muhimmancin kare jama’a farar hula, musamman al’ummar Kirista masu rauni, da kuma ɗaukar matakin hukunta masu aikata tashin hankali.

Ɓangarorin biyu sun sake tabbatar da aniyar su ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar yaƙi da ta’addanci, ciki har da aiki tare ta fannin ayyukan haɗin gwiwa na aiki, samun damar amfani da fasaha, yaƙi da safarar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba, hana tallafa wa ta’addanci da kuɗi, da gina ƙarfin hukumomin tsaro da bincike.

Tawagar Amurka ta gode wa Nijeriya bisa matakan gaggawa da ta ɗauka na ƙarfafa tsaro ga al’ummar Kiristoci da ke cikin haɗari, da kuma ’yan Nijeriya na dukkan addinai da rayuwar su take fuskantar barazana sakamakon tashin hankali da ta’addanci.

An yanke shawarar cewa za a gudanar da taro na gaba na Guruf ɗin Aikin a Amurka, a wata ranar da ta dace da ɓangarorin biyu, wadda za a tsara ta hanyar hanyoyin diflomasiyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *