Gwamnatin Tinubu ta samar da Sabbin Jiragen Yaƙi Guda 60 Don Yaƙar Ta’addanci a Najeriya

Shugaban Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Hassan Abubakar, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sayo jiragen yaki 60 domin ƙarawa rundunonin tsaro ƙarfi wajen yaki da ‘yan ta’adda a Najeriya.

Air Marshal Abubakar ya bayyana hakan ne a wajen taron Sir Ahmadu Bello Foundation da ya gudana a Arewa House a Kaduna.

A cewarsa, wannan yunkuri na daga cikin muhimman sauye-sauye da gwamnatin ke yi don tabbatar da zaman lafiya da kuma murkushe ‘yan ta’adda a sassan ƙasar.

“Gwamnatin Shugaba Tinubu ta ba mu cikakken goyon baya. Za mu yi amfani da sabbin jiragen yaki wajen kai farmaki a duk inda barazana ke fitowa. Wannan wani sabon babi ne a kokarin dawo da kwanciyar hankali a Najeriya,” in ji Air Marshal Abubakar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *