Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Sakkwato ta amince da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke na yin watsi da ƙarar da tsohon Gwamna Bello Matawalle ya shigar inda ya ke ƙalubalantar hukuncin cewa motocin da ya kwashe bayan an kayar da shi a zaben 2023 mallakin sa ne.
Idan dai za a iya tunawa, a watan Yunin 2023, bisa ƙorafin gwamnatin jihar Zamfara, ‘yan sandan jihar Zamfara sun kai samame gidan tsohon Gwamna Matawalle, inda suka ƙwace motoci sama da 40 waɗanda Matawalle da muƙarraban sa suka yi awon gaba da su kafin miƙa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce, kwamitin mutane uku na Kotun Ɗaukaka Ƙara, a wani hukuncin da Mai Shari’a Hon. A.M Talba ya yanke a ranar 08 ga Agusta 2025, ya yi watsi da ƙarar Bello Matawalle.
A cewarsa, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ɗaukaka ƙara mai lamba CS//S/2024, tsakanin Bello Muhammed Matawalle da ’Yan Sandan Nijeriya da Wasu, inda ta ce hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Sakkwato ta yanke kan haƙƙin ‘yan sanda na bincikar zargin aikata laifi daidai ne.
Ya kuma ƙara da cewa, Matawalle ya ƙasa gabatar da sahihan hujjoji da ke tabbatar da iƙirarin mallakar motoci guda 40 da aka ƙwato daga gidansa, waɗanda za su tabbatar da cewa lallai an keta masa haƙƙinsa na mallakar dukiya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A watan Yunin 2023, gwamnatin jihar Zamfara ta baiwa tsohon gwamna Bello Matawalle da mataimakinsa wa’adin kwanakin aiki biyar su dawo da duk motocin da aka sace.
“Sai dai duk ƙoƙarin ƙwato waɗannan motocin bai yi nasara ba, lamarin da ya sa gwamnatin jihar Zamfara ta nemi kotu ta bayar da umarni, inda bayan an bada umarnin ne ‘yan sanda suka ƙwato motoci sama da 40.
“Bayan an ƙwato motocin ne Bello Matawalle ya garzaya babban kotun tarayya da ke Gusau, inda kotun ta bayar da umarnin a mayar masa da motocin, haka kuma ya shigar da ƙara na daban a wannan kotun, inda ya nemi a tabbatar masa da hakƙinsa na mallakar kadarorin ciki har da motocin da ake magana a kai.
“Gwamnatin jihar Zamfara ta buƙaci a mayar da shari’ar zuwa babbar kotun tarayya da ke Sakkwato.
“Babban kotun tarayya da ke zaman shari’a a Sakkwato ta yi watsi da ƙarar a watan Disamba 2023, kuma ta ƙi yarda da maganar Bello Matawalle, saboda haka motocin ana ɗaukar su a matsayi mallakin gwamnatin jihar Zamfara ne.
Bai gamsu da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke ba, Bello Matawalle ya garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara.
“Kotun Ɗaukaka Ƙara a ranar Juma’ar da ta gabata ta amince da dukkanin hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Sakkwato ta yanke, inda ta tabbatar da cewa ‘yan sanda na da hurumin bincikar zarge-zargen da ake yi na aikata wani laifi bayan an samu ƙara.
“Ya ƙara da cewa, duk tsarin da gwamnatin jihar ta bi wajen ƙwato motocin da aka sace ya dace da doka, don haka bai saba wa haƙƙin Bello Matawalle ba, kamar yadda ake zargi, don haka babu wata burga da za ta iya kare shi daga bincike da gurfanar da shi a gaban kotu.