KWAMANDAN ISWAP IBN ALI YA MIKA WUYA BAYAN DA SOJOJIN NAJERIYA SUKA HALLAKA ‘YAN TA’ADDA DA DAMA A BORNO

Sojojin Najeriya sun sake samun nasara a fagen yaki da ta’addanci, yayin da babban kwamandan ‘yan ta’addan ISWAP, Ibn Ali, ya mika wuya tare da ajiye dukkan makamai da alburusai dake hannunsa. Wannan nasarar ta faru ne a Bama, Jihar Borno, yayin da dakarun Operation Hadin Kai ke ci gaba da matsa wa ‘yan ta’adda lamba a yankin Arewa maso Gabas.

A cewar kakakin rundunar tsaro ta kasa, Manjo Janar Markus Kangye, dakarun sun gudanar da jerin hare-hare daga ranar 4 zuwa 10 ga watan Yuli, a wurare da dama kamar su Platari, Dajin Sambisa, da Timbuktu Triangle, inda suka hallaka daruruwan ‘yan ta’adda. A cikin wannan lokaci, mata da maza da yara daga cikin ’yan ta’addan da suka karaya sun mika wuya ga dakarun Najeriya, suna neman gafara da aminci.

Bayan haka, an samu nasarar ceto mutane hudu da aka sace, da kama wasu masu taimaka wa ‘yan ta’adda guda biyar. Haka kuma, an kwato makamai da alburusai masu yawa, tare da tarwatsa wasu bama-bamai da kuma kwato kuɗaɗe daga hannun ‘yan ta’addan.

Wannan lamari na nuni da yadda hadin gwiwar dakarun Najeriya da sauran hukumomin tsaro ke haifar da gagarumar nasara a yankunan da ake fama da rikici.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *