Manufar ƙarfafa jarin bankuna shi ne inganta tsarin hada-hadar kuɗaɗe da bunƙasa ƙarfin tattalin arzikin ƙasa zuwa Dala Tiriliyan Ɗaya -CBN

Ashafa Murnai Barkiya

Babban Bankin Nijeriya ya jaddada cewa babbar manufar tilasta wa bankunan kasuwanci su ƙarfafa jarin su shi ne, domin a ƙara inganta tsarin hada-hadar kuɗaɗe, ta yadda tattalin arzikin Nijeriya zai dangane zuwa Dala Tiriliyoyan 1 nan da shekarar 2030.

CBN ya bayyana haka a yayin da manya da ƙananan bankuna ke ci gaba da ƙoƙarin ganin sun cika sharuɗɗan mallakar adadin kuɗaɗen ƙarfin jarin da aka gindaya wa kowane banki a ƙasar nan.

Mataimakin Gwamnan CBN, Mai Kula da Nagartar Tsarin Hada-hadar Kuɗaɗe, Philip Ikeazor ne ya bayyana haka, a yayin wani taron Kungiyar Manyan Manajojin Hulɗa da Jama’a na Bankuna, inda ya bayyana:

Wajibcin Bankuna Su Faɗaɗa Bai Wa Masu Ƙanana da Matsakaitan Sana’o’i Lamuni: Ya ce hakan hanya ce da za ta ƙara samar da aikin yi da kuma hada-hadar kasuwancin da zai ci gaba da bunƙasa tattalin arziki.

Ƙara Yawan Masu Buɗe Asusun Ajiyar Kuɗaɗe Kuɗaɗe: Akwai buƙatar ci gaba da ƙara yawan masu ajiyar kuɗaɗe a asusun bankuna, musamman mata ta hanyar samar masu da damar kuɗaɗen Kasuwanci, musamman a yankunan karkara.

Dalilai Na Bunƙasa Jari A Fannin Fasahar Ƙirƙire-ƙirƙiren Zamani: Akwai buƙatar bunƙasa hada-hada a tsarin fasahar sadarwa da fasahar ƙirƙire-ƙirƙiren zamani, wato AI domin sauƙaƙa gudanar da ayyuka a ko’ina.

Saboda haka Ikeazor ya ce ta hanyar da za a fi auna nasarar shirin ƙarfafa jarin bankuna shi ne samun nasarar waɗannan tsare-tsare.

Tun cikin ƙarshen watan Satumba ne dai CBN ya bayyana cewa bankuna 14 sun cika sharuɗɗan ƙarfin jarin Naira biliyan 500 da CBN ya gindaya.

A wancan lokacin, Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Olayemi Cardoso ya bayyana cewa zuwa yanzu manyan bankuna 14 ne suka cika sharaɗin tabbatar da cewa ƙarfin jarin kowanen su kada ya gaza kai Naira biliyan 500.

Cardoso ya bayyana haka ne a ranar, yayin zantawa da manema labarai bayan kammala taron kwanaki biyu na Kwamitin Ƙwararrun Mashawartan Tattalin Arzikin Ƙasa, a Abuja.

Tun cikin watan Maris ne dai CBN ya kafa sharaɗin cewa duk wani babban bankin da ke da rassa a ƙasashen waje, tilas mafi ƙanƙantar jarin sa ya kasance Naira biliyan 500 lakadan ba ajalan ba.

A taron na ranar Talata, wanda shi ne na 302 da CBN ya shirya, tun bayan kafa bankin, Cardoso ya yi kira ga bankunan kasuwanci su ci gaba da hoɓɓasan ƙarfafa jarin su, domin kai ga nasarar bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Har ila yau a wurin taron dai Babban Bankin Nijeriya ya rage kuɗin ruwan da bankuna ke caza daga kashi 27.5 zuwa kashi 27.

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana rage kuɗin ruwa, daga kashi 27.5 zuwa kashi 27.

Gwamnan CBN Olayemi Cardoso ne ya bayyana haka, a ranar Litinin jim kaɗan bayan kammala taron Kwamitin Ƙwararrun Bada Shawarwari kan Tattalin Arziki (MPC), a Abuja.

Cardoso ya ce kwamitin ya amince a rage kuɗin ruwa da ɗigo .50, wato daga kashi 27.5 bisa 100, ya koma kashi 27 bisa 100.

Wannan ne dai karo na farko da adadin gejin kuɗin ruwa ya yi ƙasa, wato mafi ƙaranci a cikin shekaru biyar.

Gwamnan na CBN ya ce an yanke shawarar rage kuɗin ruwan ne domin ci gaba saukar malejin tsadar rayuwa da na hauhawar farashi, wanda tsawon watanni biyar kenan ake samu a jere.

Dama masara sun yi hasashen cewa malejin tsadar rayuwa zai ƙara yin ƙasa sosai a sauran watannin ƙarshen 2025.

Haka kuma wani dalilin rage kuɗin ruwan shi ne domin a ci gaba da ƙarfafa tattalin arziki.

Wannan ragin kuɗin ruwa da CBN ya yi wanda bankuna za su riƙa cajin masu karɓar ramce, ya zo ne daidai lokacin da ita kuma Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce tattalin arzikin Nijeriya ya ƙaru da kashi 4.23 cikin ɗari a darajar GDP a zango na biyu na shekarar 2025, idan aka kwatanta da shekarar 2024.

Hukumar ta bayyana haka ne a cikin rahoton GDP na Nijeriya na zango na biyu na shekarar 2025 da ta fitar a Abuja, a ranar Litinin.

Rahoton ya nuna cewa wannan ci gaban ya fi kashi 3.48 da aka samu a zango na biyu na 2024, haka kuma ya fi kashi 3.13 da aka samu a zangon farko na 2025.

Zuwa ciki watan Nuwamba ɗin nan ana ƙara samun yawan bankunan da ke cika sharuɗɗan ƙarfafa yawan jarin su. Ko cikin makon da ya gabata sai da CBN ya shawarci bankunan da ba su iya cika sharuɗɗa su haɗe da wasu wato su yi maja domin ƙarin ƙarfi, ko kuma su rage ƙarfin gejin lasisin su.

A ƙa’ida dai CBN na so manyan bankuna masu rassa a ƙasashen waje ya kasance ƙarin jarin kowanen su ya kai Naira biliyan 500. Su kuma manyan bankunan da iyakar ƙarfin su cikin gida ne, to kada ƙarfin jarin su ya gaza kai Naira biliyan 200.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *