A matsayin wani ɓangare na taron kowane kwata na Ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC (Progressive Governors’ Forum) tare da Kwamishinonin Yada Labarai daga jihohin da jam’iyyar APC ke mulki, Mai Girma Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya jagoranci Kwamishinonin wajen ziyartar tashar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana mai ƙarfin 12 Megawatt (12MW Hybrid Solar Plant) da Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Yankunan Karkara (Rural Electrification Agency – REA) ta gina a Jami’ar Maiduguri.
Wannan babban aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana ba wai kawai yana bai wa Jami’ar Maiduguri da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri wuta ba, har ma ya taimaka wajen rage katso mai yawa na kuɗin da jami’ar ke kashewa a baya wajen samun makamashi.
