NELFUND ta buɗe tsarin neman lamunin ɗalibai na shekarar karatu ta 2025/2026

Hukumar Lamunin Ilimi ta Najeriya (NELFUND) ta sanar da buɗe shafin yanar gizo na neman lamunin dalibai na shekarar karatu ta 2025/2026, domin bai wa dalibai a fadin ƙasar damar samun tallafin kuɗi don ci gaba da karatu.

Manajan Daraktan hukumar, Akintunde Sawyerr, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Daraktar Hulɗa da Jama’a na NELFUND, Oseyemi Oluwatuyi, ta fitar a ranar Talata a Abuja. A cewar sanarwar, za a buɗe tsarin neman lamunin daga Alhamis, 23 ga Oktoba, 2025 zuwa Asabar, 31 ga Janairu, 2026, wanda zai rufe cikakken zangon karɓar sabbin dalibai na wannan shekarar ta karatu.

Sawyerr ya gode wa makarantun gaba da sakandare bisa haɗin kai da suka bayar tun farkon fara shirin, tare da kira gare su da su ci gaba da ba da goyon baya domin tabbatar da tsarin lamunin ya kasance mai sauƙi, gaskiya, da shigar da kowa, musamman sabbin dalibai da waɗanda suka dade suna karatu. Ya tunatar da makarantu su sabunta bayanan daliban su a a shafin tantance ɗalibai (Student Verification Portal), domin ba da damar da dalibai za su iya neman lamuni ba tare da matsala ba.

Ya ce daidaitattun bayanan makarantu na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da cewa dalibai sun sami damar amfana da shirin lamunin, yana mai cewa sabbin dalibai za su iya amfani da lambar JAMB ko takardar shiga makaranta maimakon lambar rajista yayin neman lamuni. Ya kuma roƙi makarantu su sassauta wa dalibai da ke jiran kuɗin lamuni wajen biya da rijista, don kada rashin kuɗi ya hana su ci gaba da karatu.

Sawyerr ya ƙara da cewa makarantu da ba su fara zangon karatun 2025/2026 ba, su aika jadawalin karatunsu zuwa hukumar NELFUND domin daidaita lokacin biyan lamunin. Ya kuma bukaci su samar da hanyoyin rajista na wucin gadi ga daliban da ke jiran amincewa daga hukumar, domin kada wani dalibi da ya cancanta ya gaza samun damar karatu saboda jinkirin kuɗi.

“Don neman taimakon karin bayani, makarantu za su iya tuntuɓar NELFUND ta adireshin imel ɗin: data@nelf.gov.ng,” in ji Sawyerr.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *